Xi Jinping: Za mu ragargaza masu son raba China

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Xi Jinping ya yi wani gargadi mai tsauri ga masu zanga-zanga a Hong Kong.
Shugaban ya ce dukkan wani yunkurin raba China zai gamu da abin da ya kira "ragargaza ga wadanda suka nemi yin haka".
Shugaban yayi furta wadannan kalaman ne a yayin wata ziyara da ya kai kasar Nepal a ranar Lahadi, kamar yadda tashar talabijin mallakin gwamnatin China wato CCTV ta ruwaito.
A ranar Lahadin ne kuma zanga-zangar ta kazance, inda har ya sauay zuwa fito-na-fito tsakanin masu rajin kawo sauyi da 'yan sanda a Hong Kong.
An lalata tashoshin jirgin kasa da shagunan da ake zargi masu su na goyon bayan China ne a lokacin zanga-zangar ta baya-bayan nan.
Kuma a bangarorin birnin Hong Kong, an gudanar da zanga-zanga, wadda ta kai ga rufe tashohi 27 na jiragen karkashin kasa na HK mai suna MTR.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wani rahoto da ke cewa wasu masu sayayya a wani katafaren shago sun kori 'yan sanda daga ginin bayan da suka nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar.

Asalin hoton, EPA
An dai fara wadannan jerin zanga-zangar ne a watan Yuni bayan da hukumonin birnin suka nemi saka wata doka da za ta ba su damar mika masu laifi kai tsaye zuwa China domin a hukunta su.
Amma duka janye kudurin dokara da a ka yi, masu rajin kare hakkin jama'ar birnin Hong Kong sun fadada bukatunsu - wadanda a yanzu sun hada da samar da cikakken 'yanci na siyasa da binciken jami'an tsaro da ake zargin aikata laifukan azabtar da masu zanga-zangar.
Fiye da mutum 2300 hukumomi suka damke tun da tashin hankalin ya fara.











