Za mu ceto mutum 9 da aka sace a Abuja - 'Yan sanda

Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, ta ce tana daukar duk matakan da suka dace wajen ceto mutum 9 da aka yi garkuwa da su ranar Litinin a kauyen Pegi da ke yankin Kuje ta Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, DSP Anjuguri Manzah, ta ce rundunar na iya bakin kokarinta wajen ganin ta sada mutanen da iyalansu a saboda haka jama'a su kwantar da hankalinsu.

An dai sace mutanen ne da misalin karfe 8 na daren Litinin, inda wasu mutane sanye da kayan sojoji suka yi awon gaba da su.

Wata mata Mrs Sharon Alfred da mijinta ke cikin wadanda aka sace din ta tabbatar wa BBC faruwar lamarin, inda kuma ta ce sun kira lambar maigidan nata inda ya ce musu shi da sauran mutanen na hannun masu garkuwar.

"Ya ce mana sun yi tafiya mai nisan gaske kuma a yanzu haka bai gane inda aka ajiye su ba, sannan kuma mutanen sun ce sai an ba su miliyan 10 kafin su sake su."

BBC ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda na birnin tarayya Abuja, Anjuguri Manza don jin halin da ake ciki amma ya ce a yanzu ba ya gari don haka ba shi da tabbacin faruwar lamarin.

Wakilin jaridar Daily Trust da lamarin ya faru a kusa da gidansa Muideen Olaniyi, ya ce 'yan bindigar sun yi harbi kan wasu motoci biyu kirar Nissan Frontier da Toyota Solara.

Ya kuma ce daya daga cikin wadanda ke cikin motocin na cikin mawuyacin hali.

'Yan bindigar sun saki daya daga cikin wadanda suka sacen saboda rashin lafiya, kuma ya shaida wa dan jaridar cewa maharan duk matasa ne.

Rahotanni sun ce masu garkuwa da mutanen sun kira daya daga cikin 'yan uwan wadanda aka sacen kuma sun bukaci a biya naira miliyan 10 kafin a sako mutanen.

Wakilin Daily Trust din ya ce wannan ne karo na biyu da ake garkuwa da mutane a unguwar Pegi din, don a bara ma an yi garkuwa da mutane hudu a unguwar.

A watan da ya gabata ne dai shugaban 'yan sandan kasar, Mohammed Adamu, ya ce Abuja na daga cikin wurare mafiya karancin miyagun laifuka a duniya.

Wannan furuci da shugaban 'yan sandan ya yi ya sa BBC ta gudanar da wani bincike don gano gaskiyar kalaman nasa, kuma binciken ya gano cewa zancen ba haka yake ba.