Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hikayata: Alkalai sun fara aikin fitar da gwarzuwa
Tuni alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, suka fara aikin fitar da labarai uku da suka ciri tuta a bana a yau Talata.
Daga cikin wadannan labarai uku ne kuma za a zabi labarin da zai hau matsayi na daya a gasar.
"Wani muhimmin bambanci tsakanin gasar bana da ta baya", a cewar mukaddashin Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, "shi ne a bana sai ranar da za a karrama gwarzuwar gasar za a fadi sunan wacce ta yi nasara.
"Domin haka ko wacce daga cikin marubutan da labarin ta ya kai wannan mataki za ta iya kasancewa Gwarzuwar Gasar".
Tantancewa
Labarai sama da 300 ne dai aka shigar gasar ta Hikayata ta bana, kuma kafin a kawo wannan mataki sai dai aka tankade aka kuma rairaye labaran zuwa 30.
Wajen tantancewar dai an yi amfani da ka'idojin shiga gasar, musamman game da adadin kalmomi, da bin ka'idar rubutu, da amfani da daidatacciyar Hausa, da kauce wa amfani da kalaman da ba su dace ba da zarge-zarge, da ma tabbatar da cewa labarin kagagge ne.
A mataki na gaba kuma, inda aka sake rairaye labaran, aka fitar da guda 25 (duba teburin da ke kasa), wadanda aka turawa alkalan gasar su uku don zabo su, kuma su darzo wadanda suka fi cancanta.
Labarai 25 da alkalai suka tantance
- Kaddarata
- Duniyarmu
- Hattara Dai Iyaye
- Kura da Shan Bugu
- Ishara
- Ranar Salla
- Menene Laifina
- Maza Mutanenmu
- Cin Amana
- Zahra
- Hansatu 'Yar Baiwa
- Mugunyar Kawa
- Nadama
- Kaddarar Rayuwa
- Maraici
- A Juri Zuwa Rafi
- Bakin Alkalami
- Gaba ta Wuce
- Cikar Buri
- Da Guminmu
- Rudin Duniya
- Ba a Yi Komai Ba
- Awa Arba'in da Takwas
- Abin da Ka Shuka
- Zamanin da Nake Raye
Dukkan labaran 15 dai za a karanta su nan gaba a rediyo a kuma saka su a shafukanmu na intanet da na sada zumunta.
Wace ce za ta zama Gwarzuwar Hikayata ta bana?
A karshen watan nan na Oktoba ne dai ake sa ran za a sanar da Gwarzuwar Hikayata ta 2019 yayin wani bikin karrama wadanda suka yi nasara a Abuja, babban birnin Najeriya.
Duk wacce labarinta ya zo na daya za ta samu kyatutar kudi dalar Amurka 2,000 da lambar yabo; wacce ta zo ta biyu za ta wuce da kyautar kudi dala 1,000 da lambar yabo; yayin da mai matsayi na uku za ta karbi kyautar kudi dala 500 da lambar yabo.
Wannan ce shekara ta hudu ta gasar, kuma a cewar Malam Aliyu Tanko, shiga gasar da mata suka yi daga sassa daban-daban na duniya na "nuna yadda iyayenmu mata ke da shaukin yin rubutu da ma shiga wannan gasa."Baya ga labarai ukun da alkalan za su zaba, za su kuma fitar da wasu 12 wadanda suka cancanci yabo.
A bara dai Safiyya Jibrin Abubakar ce ta lashe gasar da labarinta mai suna "'Ya Mace", wanda ya yi shagube a kan halin da 'ya'ya mata kan fada a tsakanin al'umma.