Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
#RevolutionNow: Kotu ta umarci a ci gaba da tsare Sowore
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS da ta ci gaba da tsare Mista Omoyele Sowore, wato mutumin da shirya zanga-zangar #RevolutionNow da ke kira da a yi juyin juya-hali, har tsawon kwana 45.
Mista Sowere wanda ya yi takarar shugabancin Najeriya a babban zaben watan Fabrairun bana, an kama shi ne a makon jiya bayan ya fara kirayen-kirayen zanga-zangar.
Kotun ta ce ta yanke wannan hukuncin ne domin 'yan sanda su samu damar kammala binciken da suke yi a kansa da kuma yiwuwar tuhumarsa.
'Yan sanda sun bayyana kiraye-kirayen juyin juya halin da ya yi da "cin amanar kasa da kuma aikin ta'addanci".
A ranar Litinin ne dai aka fara zanga-zangar a birnin Legas, sai dai mutane kalilan ne suka halarci tarukan a fadin kasar.
Abin da ya jawo 'yan sanda suka kama wasu daga cikin masu zanga-zangar.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi Allah-wadai da kama masu zanga-zangar da kuma Sowore, wanda shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters.
Kuma kungiyoyin sun bayyana kamen da take hakkinsu na yin zanga-zangar lumana.