Trump ya yi barazanar lalata tatalin arzikin Turkiyya

Lokacin karatu: Minti 3

Amurka ta ya yi barazanar gurgunta tattalin arzikin Turkiyyan idan Turkiyyar ta wuce ka'ida.

Shugaba Trump ne ya yi gargadin bayan sanar da janyewar dakarun Amurkan daga Arewa-maso-gabashin Syria ba zato, ba tsammani.

A jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Trump ya kare matakin da ya dauka, wanda ke iya ba Turkiyya damar kai wa mayakan Kurdawa hari a makwabciyarta Syria.

Janye dakarun ya jawo wa Trump kakkausan suka daga magoya bayansa 'yan jam'iyyar Republican.

Mayakan Kurdawa na daga cikin manyan abokan Amurka da suka taimaka mata wurin murkushe mayakan kuniyar IS.

Amma Turkiyya na daukar mayakan Kurdawan a matsayin 'yan ta'adda.

Amurka ta girke dakaru sama da 1,000 a Syria. An janye kimanin 24 daga cikin sojojin daga iyakokin Syria, kamar yadda wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana,

Mene ne matsayin shugaba Trump?

A ranar Litinin shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na Tuwaita cewa an an zabe shi ne domin ya "fitar da kasar daga wannan yakin da ya ki karewa. Yanzu Turkiya da nahiyar Turai da Syria da Iraki da Rasha da Kurdawa ne za su lalubo mafita daga matsalar."

Hakan ya biyouy bayan hirar wayar da yi da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya. Bayan hakan ne fadar White House ta ce Turkiyya za ta "kai hare-haren da ta dade da tsarawa a arewacin Syria, kuma sojojin ba za su kasance a yankin ba".

Bayan Kurdawan sun zargi Amurka da cin amana da kuma suka daga 'yan siyasar kasar, Trump ya kara wallafa jerin wasu sakonni a ranar Litinin, yana jan kunnen Turkiyya idan har ta kuskura ta yi wani wani abu, to zai karya tattalin arzikinta.

A bara, Amurka ta kara haraji a kan wasu kayan da Turkiyya ke samarwa kuma ta kakaba takunkumi a kan wasu manyan jami'an Turkiyya bayan an samu rashin jituwa tsakanin kasashen biyu na kungiyar NATO.

A gargadinsa ga Turkiyya, Trump ya ce kada Turkiyya ta sake ta yi wani abin da Amurka ke ganin rashin imani ne. Shugaban Amukan ya ce idan har aka cutar abokan nasu, to za a samu babbar matsala.

A cikin wata sanarwa, kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Jonathan Hoffman ya ce "ma'aikatar ta yi wa Turkiyya magana da babbar murya cewa Amurka ba ta amince da matakin da Turkiyya za ta kai a Yammacin Syria ba".

Me Turkiyya za ta yi a Syria?

A taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, Shugaba Erdogan ya gabatar da taswirar wani yanki mai fadin kilomita 480 da ba a yaki a iyakar Syria da yake so kasarsa ta kula da shi.

Yankin zai zama matsuguni ga 'yan Syria kimanin miliyan 3.6 da ke zaman gudun hijira a Turkiyya.

A ranar Litinin ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce "an kammala dukkanin shirye-shirye domin daukar matakin," kuma kafa irin wannan yankin na da "muhimmanci" ga 'yan Syria da kuma samar da aminci a yankin.

Sai dai Turkiyya ta sha yin barazanar kai hari a kan mayakan Kurdawa a iyakokin Arewa-maso-yammacin Syria.

Turkiyya na daukar 'yan sa kan Kurdawa na YPG a matsayin wani reshe na haramtacciyar kungiyar Kurdawa da ta kwashe shekara 30 tana neman ballewa daga Turkiyya.

A wani bangare kuma a ranar Talata Iran ta bayyyana adawarta da duk wani matakin soji da Turkiyya za ta dauka a Syria.

Mayakan SDF na gudanar da wasu sansanonin 'yan gudun hijira da na rike iyalen wadanda ake zargin mayakan kunigyar IS ne a ciki da wajen yanki mai amincin da Turkiyya ke bukata.

Ana rike da iyalen wadanda ake zargi mayakan IS a Ain Issa da Roj da ke cikin yankin.

Sansani mafi girma shi ne na Al-hol, da ke kusa da iyakar Iraki, kuma yake da nisan kilomita 60 daga Tukiya. Mutane 70,000 ne ke sansanin Al-hol, kashi 90 dinsu mata da kananan yara ne, wadanda suka hada da mutum 11,000 'yan kasashen ketare.