Sanata Rochas ya bukaci a zabtare yawan sanatocin Najeriya

Dan majalisar dattawan Najeriya Sanata Rochas Okorocha ya yi kira a rage yawan 'yan majalisar dokokin kasar da zummar kawo karshen kashe kudin gwamnati babu gaira babu dalili.

Sanata Rochas, wanda tsohon gwamnan jihar Imo ne, ya bayyana wannan matsayi ne a zauren majalisar ranar Alhamis.

Ya ce "tsarin mulkin Najeriya ya bukaci a samu Sanata uku daga kowacce jiha. Ina ganin hakan bata kudi ne. Don haka ya kamata a kowacce jiha a samu sanata guda daya. Mene ne amfanin sanatoci masu yawa? Mene ne amfanin 'yan majalisar dokoki fiye da dari uku?"

A halin da ake ciki dai sanatoci 109 ne a majalisar dattawan kasar, yayin da ake da 'yan majalisar dokokin tarayya 360.

Hakan na nufin kowace jiha na da sanatoci uku.

Yawan 'yan majalisar dai yana tasiri sosai kan tattalin arzikin kasar, ganin cewa ana kashe biliyoyin naira domin gudanar da harkokinsu.

'Yan Najeriya sun sha kokawa kan makudan kudin da ake kashe wa 'yan majalisar, suna masu cewa kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.

Ko da a kwanakin baya sai da 'yan kasar suka bayyana bacin ransu bayan majalisar dattawan ta nuna aniyarta ta kashe N5.550 bn domin saya wa mambobinta motocin alfarma.