Wani ya kai karar kamfanin Apple kan mayar da shi dan luwadi

Asalin hoton, Getty Images
Wani mutum dan kasar Rasha ya kai karar kamfanin Apple masu wayar Iphone kan zargin wata manhajarsu da ta mayar da shi dan luwadi.
Ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon wata manhaja mai suna ''Gaycoin'' wacce manhaja ce da ake hada-hadar kudade ta intanet da ita.
Ya ce manhajar ta rikita masa tunani inda yanzu yake bukatar fam dubu 12 a matsayin diyya, kamar yadda wata takardar koke da kamfanin dillancin labarai ta AFP ta gani.
An hallarta luwadi a Rasha tun 1993 amma har yanzu ana nuna musu wariya.
A 2013, majalisar dokokin Rasha ta amince da wata doka inda ta hana yada abin da ta kira ''farfagandar 'yan luwadi.''
Mene ne asalin abin da ya faru?
A karar da ya kai a ranar 20 ga watan Satumba, ya yi zargin cewa ya nemi saka manhajar ''bitcoin'' a wayarsa inda ya ga wata daban mai suna 'gaycoin.'
Kamar yadda ya bayyana, manhajar da ta shiga wayarsa ta rubuta masa ''kada kayi hisabi sai ka gwada.''
Wannan dalili ne yasa shi tunani kan gwada shiga luwadi.
Ya bayyana cewa yanzu haka ya fada wannan harkar kuma iyayensa basu sani ba kamar yadda ya bayyana a takardar koken.
Ya ce bai ji dadin faruwar hakan ba sakamakon ba zai taba koma wa yadda yake ba.
Har yanzu kamfanin Apple bai ce komai kan zargin ba.











