Gaske ne Boko Haram ta sake kashe sojoji a Borno?

ISWAP

Asalin hoton, Getty Images

Bayanai daga Najeriya na cewa kungiyar Boko Haram ta hallaka akalla mutum 9 a wani hari da ta kai garin Gubio da ke jihar Borno.

Kamfanin dillanci labarai na Rueters ya ce an kai harin ne a yammacin Lahadi inda kuma aka kai har zuwa daren ranar suna cin karensu babu babbaka.

Kafar ta Reauter ta sake wallafa rahoto a ranar Litinin cewa kungiyar IS ta fitar da ikrarin cewa ta kai harin kuma ta kashe da jikkata sojoji da dama.

Rundunar Lafiya Dole mai yaki da kungiyar Boko Haram din ta tabbatar da kai harin, sai dai ta ce ba kamar yadda ake bayar da rahoto ba.

Birgedia Janar Adesino Olusegun wanda shi ne shugaban rundunar Lafiya Dole din ya shaida wa BBC cewa ya ziyarci garin Gubio da yammacin ranar Litinin din nan, inda ya ce dakarunsu sun dakile harin na Boko Haram na ranar Lahadi.

Ya kara da cewa sojojin nasu sun samu nasarar fatattakar 'yan Boko Haram tare da kwace makamansu bayan kashe wasu daga cikinsu duk da cewa bai fadi adadinsu ba.

Sai dai kuma da aka tambaye shi ko 'yan kungiyar sun kashe sojoji? Sai ya ce "ku jira bayani daga mai kula da rundunar, kanal Isa Ado."

Kamfanin dillanci Labarai na Reuters a farkon watan nan ya rawaito cewa mazauna garin Gubio sun ce sun ga mayakan Boko Haram da suka yi wa kungiyar IS mubaya'a sun wuce ta garin nasu.

An dai ce mayakan sun tsaya a garin na Gubio inda suka ja al'ummar garin sallah.