Mutum 4 sun mutu bayan kwalekwale ya kife da su a Sengal

Gabar ruwa a kasar Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ci gaba da neman sauran mutanen da hadarin kwalekwalen ya rutsa da su a ranar Talata

Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu a gabar ruwan Dakhar babban birnin kasar Senegal.

An kai wasu mutum 35 daga cikin fasinjojin kwalekwalen asbiti, yayin da ake ci gada da aikin neman sauran fasinjojin.

Hukumar bayar da agaji ta kasar ta ce kwalekwalen ya kife ne sakamakon wata mahaukaciyar guguwa a daren Litinin.

Hukumar ta shaida wa BBC cewa fasinjojin na kan hanyarsu ta zuwa yawon bude ido ne a tsibirin Madeleine, duk da cewa an samu gargadin rashin kyan yanayi.

Jami'an hukumar sun ce fasinjojin sun hada da Faransawa shida, Jamusawa biyu, da 'yan kasar Sweden biyu da kuma mutum daya dan kasar Guinea Bissau.

Laftanar Kanar Pape Ange Michel Diatta, ya ce duk da cewa babu tabbacin musabbabin hatsarin, akwai yiwuwar ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi ne suka sa kwalekwalen kifewa.

Zuwa lokacin da ake hada rahoton, ba a san kasashen da hudu daga cikin wadanda suka rasu a hatsarin suka fito ba.

Taswirar kasar Senegal
Bayanan hoto, Taswirar kasar Senegal