Haduran da karuwai ke fuskanta a Malawi

'Yar jarida mai daukar hoto, Isabel Corthier ta tattauna da mata masu zaman kansu da suka kasance a wani shirin sama wa mata masu zaman kansu lafiya a kudancin Malawi.

Two women

Asalin hoton, Isabel Corthier

Kasar Malawai na daya daga cikin kasashen da suke da yawan masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki da mata masu zaman kansu da suke da yiyuwar kamuwa da cutar.

Adadin matan da suke samun juna biyu kafin aure da cututtukan da ake samu ta hanyar saduwa na karuwa a kasar.

Tun shekarar 2014, kungiyar likitoci ta kasa da kasa, Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ke aiki kafada da kafada da ma'aikatar lafiya ta Malawi da sauran kungiyoyi wajen inganta lafiyar mata masu zaman kansu.

Har wa yau, kungiyar na ba su damar samun kwaroron roba ba tare da wani shamaki ba da wani magani, PEP da ke rage yiyuwar kamuwa da cutar HIV.

Ms Corthier ta dauki hotunan wasu mata da suke wannan sana'a, sai dai ta boye ainihin sunayensu.

Wata jami'a daga kungiyar MSF, Kate Ribet ta yi hira da su kan abin da ya jefa su wannan sana'a. Kate ta kuma yi hira da wasu da ga cikin ma'aikatan kungiyar likitocin.

An sauya sunayen masu zaman kan nasu domin a boye ainihin sunayensu.

Presentational grey line

Yadda Bernadette ta tsinci kanta a sana'ar a Dedza

Photo of Bernadette

Asalin hoton, Isabel Corthier

Bernadette, ta taso ne cikin 'yan uwanta 11. Ta rasa iyayenta a lokacin tana shekara bakwai inda ta girma a hannun yayarta daga baya ta koma hannun kakanninta.

Rashin tallafi daga'yan uwanta wajen gudanar da harkokinta na rayuwa ya sa ta shiga wani hali har ta kai ga ta tsinci kanta wajen yin ban gishiri in baka manda domin ta samu ta ci abinci ko ta siyi kayan makaranta. A haka ne har Bernadette ta samu juna biyu wanda ya tilasta mata barin makaranta a lokacin tana 'yar shekara 18.

A yanzu haka, Bernadette, ta na da yara shida. Abokin rayuwarta ya jefa ta cikin halin ni-'yasu saboda yawan cin zarafinta da yake yi ya sa sai ta kara komawa zaman kanta a shekarar 2018 saboda a cewarta shi ne kawai hanyar da take ganin za ta sa ta cigaba da tafiyar da rayuwarta.

Portrait of Bernadette

Asalin hoton, Isabel Corthier

"Na ji ayyukan da kungiyar likitoci ta MSF ta yi a Nuwambar 2018 a lokacin da daya daga cikin ma'aikatan kungiyar ya je wajen shan barasa inda yake ba da bayanai kan gwajin da ake yi wa masu cututtukan da ake samu ta hanyar saduwa da cutar HIV''. In ji Bernadette.

"Wannan ne karon farko da na samu bayanai kan gwajin HIV. Kafin yanzu, ba bu abin da na sani game da haka. Na yi murna saboda a yanzu ina jin abubuwan da a baya kwata-kwata ban san da su ba''.

"A yanzu, na kara samun kwarin gwiwa a kan da kuma ina da damar da zan bukaci kariya ko yin amfani da kwaroron roba kafin hulda da abokan sana'a. Na san yadda ake sanya robar sosai sannan akwai wani mai da zai kare ni daga samun juna biyu''

Presentational grey line

Maria ma tana sana'ar zaman kai a Dedza

Portrait of Maria

Asalin hoton, Isabel Corthier

Ita kuwa Maria, 'yar shekara 36, ta shafe shekara 11 a gidan miji, ta na sayar da albarkatun gona da mai gidanta. Mijinta ya gudu ya barta bayan fuskantar cin zarafi na tsawon shekaru, A haka ta yi ta fadi ta shi domin ciyar da kanta da 'yarta har ta samu kanta a sana'ar mata masu zaman kansu.

"Wasu lokutan abokan huldata ba sa biya na ko kuma ka same su masu saurin fushi, A cewar Maria. ''Shekaru biyu da suka gabata, na samu wani kwastoma, mun yi komai amma bayan ya biya bukatarsa, sai ya ki biyana kudina''

"A lokacin da muke saduwa, da gayya ya cire kwaroron robar da ya sa. Mun yi sa-in-sa da shi kan hakan har dai ta kai ga ya cire min daya daga cikin hakorana na gaba. Daga nan kuma ya ce ba zai biyani kudin ba''

Portrait of Maria

Asalin hoton, Isabel Corthier

"Kafin kungiyar MSF ta zo nan, ana kiran mu da mata masu zaman kansu. Idan kuma muka je gaban 'yan sanda, sai su kore mu''

"Yanzu za mu iya samun magani a asibiti ba tare da wata matsala ba''

Presentational grey line

Adeline, kuwa jami'ar lafiya ce a Bangula daga kungiyar MSF

A group of women receive contraception education

Asalin hoton, Isabel Corthier

Adeline ta fara ne a matsayin jami'ar lafiya a yankinta a watan Fabrairun 2015.

''Amatsayina na jami'ar kula da lafiya, na koyi yadda zan kula da kaina domin na inganta lafiyata'' In ji Adeline.

"Sanin ilimin na nufin mutum zai iya zuwa asibiti ya samu kulawar likitoci, sannan ka yi sana'arka ta mata masu zaman kansu ka kuma tallafa wa 'yan uwanka da ma al'ummarka''.

Tun shekarar 2005 Adeline take wannan sana'a. A baya ta yi aure har ta samu 'ya'ya biyu sai dai bayan da aurenta ya mutu ne ta rasa yadda za ta kula da yaranta.

Ta ce ''Wata kawa ta same ni take ce min me ya sa nake fuskantar irin wannan rayuwa? Akwai hanyar da za ki bi ki share hawayenki. Za ki iya samun kudi idan kika koma zaman kanki'.

"Na karbi shawararta kuma da na gane cewa ina samun hanyoyin samun kudi, sai na yanke shawarar karbar wannan sana'a hannu bi-biyu''.

A group of women receive contraception education

Asalin hoton, Isabel Corthier

Sai dai irin wannan sana'a ta mata masu zaman kansu na tattare da hadarurruka. A cewar ta.

"A shekarar 2007, da dare ina aiki a Blantyre sai wasu maza suka rufe ni da kawata da duka suka kwace komai na hannunmu.

"Wata rana kuma abokin huldata ya min fyade a lokacin da yake biyan bukatarsa. Ban je wajen 'yan sanda na kai kara ba. Mutumin sananne ne a yankin kuma ya sha yi wa mata fyade sannan yana yi wa matan da suka kai kararsa barazana. Shi ya sa na ga gwara na ja bakina na yi shiru''.

Presentational grey line

Chrissie Nasiyo, ma'aikaciyar jinya ce da kungiyar MSF a Nsanje

A group of women receive contraception education

Asalin hoton, Isabel Corthier

Chrissie ta yi aiki na shekaru biyu da wadanda suke bibiyar harkokin mata masu zaman kansu.

"Mace ta fito ta iya fadin ni mai zaman kaina ce abu ne mai wahala saboda yanayi na al'ada da tsangwama da ke tattare da yin hakan''.

"Mata masu zaman kansu na iya jin wani iri idan suka fito suka bayyana sana'arsu. Wasu kuwa ba sa jin komai''.

Chrissie ta yi bayanin irin banbancin da ake samu tsakanin masu sana'ar mata masu zaman kansu a kasar Malawi.

"Akasarin mutane sun fi sanin mata masu zaman kansu a matsayin sana'a. Za ta tashi duk safiya, ta yi ado ta kuma fita farautar kwastoma''

"Amma ga mai zaman kanta wadda take aiki, tana zuwa ta yi aikinta sannan tana da abokan huldarta da dama domin samun na kashewa, ba za ta taba amincewa a kira ta mai zaman kanta ba''.

"Yi wa irin wadannan mata bayani zai taimaka musu su tantance''.

Chrissie na bai wa mata masu zaman kansu irin wadannan shawarwarin. Ana bai wa mahalarta kwaroron roba da yi musu gwajin kamuwa da cututtukan HIV da cututtukan da ake kamuwa ta hanyar saduwa wato STI da bada tazarar haihuwa.

Chrissie ta ce mafi yawan mata masu zaman kansu da take aiki da su suna dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

A woman hugging another woman

Asalin hoton, Isabel Corthier

"Ina son aiki da 'yan matan da suke wannan sana'a saboda suna da labaran da za su bayar.

''Watakila idan ka ji labarinsu, ka iya yi musu kallon suna tafka ta'asa, suna yin haka ne saboda wani dalili''

Presentational grey line

Ketisha ita ma matashiya ce mai zaman kanta a Mwanza

Portrait of Ketisha

Asalin hoton, Isabel Corthier

A lokacin da Ketisha mai shekara 16 tana makaranta , ta kasance tana soyayya da wani har ta samu juna biyu. Mahaifinta kuma ya yi watsi da ita.

Ta zauna da 'yar uwarta na wani lokaci daga bisani ta daina kwana tare da ita. Ketisha ta yi kokarin kaucewa wannan sana'a.

Ta ce ''Samun kai na a wannan sana'a ba ya na nufin ban taba gwada wasu hanyoyin da zan samu kudin kula da kai na ba ne''

'Na gwada sayar da gasasshen burodi amma abubuwa ba su tafi dai-dai ba. Bayan nan, na koma sayar da masara ita ma daga karshe ba alherin da yake fitowa ta sana'ar.

Portrait of Ketisha

Asalin hoton, Isabel Corthier

"Babu sauki a matsayina na matashiya da na tsunduma cikin wannan harka. Ina yawan shan tambaya kan ya aka yi a irin wannan shekarun nawa nake wannan harka a maimakon a ce ina makaranta. Iyayena ba su san cewa ga abin da nake yi ba.

"Idan na dudduba, da yawan matasa da ke zaman kansu na fuskantar kalubale. Ana tilasta musu saduwa da mazan da shekarunsu suka ja ba tare da yin amfani da kariya ba kuma ba tare da biyansu ba. Idan suka nemi bahasi kuma a ci zarafinsu''.

Presentational grey line

Jennifer ita ma tana gudanar da harkokinta a Mwanza

Portrait of Jennifer

Asalin hoton, Isabel Corthier

Jennifer mai shekaru 26, ta na da 'ya'ya biyu. Mijinta ya shahara wajen sata. Lokacin da ta bukace shi ya daina sace-sace, bai saurare ta ba. Hakan ya sa suka rabu.

A shekarar 2008. Jennifer ta fara tunanin hanyar da za ta taimaka mata wajen kula da 'ya'yanta shi ne ta fara zaman kanta.

"Lokacin da 'yan uwana suka samu labarin abin da nake yi, kora ta suka yi suka kuma ce ka da na sake dawowa gida'' In ji Jennifer.

''Sai dai kasancewar dan uwa dan uwa ne, daga baya na ziyarce su kuma sun yi min tarba mai kyau. A yanzu haka, 'ya'yana na zaune ne da mahaifiya ta''.

Portrait of Jennifer

Asalin hoton, Isabel Corthier

"Amatsayina na matashiya mai zaman kanta, ina fuskantar kalubale da dama. Akwai wata rana da abokin huldata ya biya kafin alkalami kuma ya zo wajena. Ya ce mini na je na siyo dankalin turawa, na je na siyo sai dai dana dawo, sai na tarar ya yashe ni, ya kwashe min kudade na da kayana.

"Ina da niyyar na daina wannan sana'a saboda abu ne mai wahala. Idan kuma har na cigaba, ina jin cewa zan mutu kafin lokaci na ya cika.