'Yan majalisar Birtaniya sun kai karar Boris Johnson

Wani alkali a Scotland na duba wata kara da wasu 'yan Birtaniya suka shigar a gabansa domin hana tura majalisar Birtaniya zuwa hutun dole.
Ya saurari hujjoji daga wakilan dukkan bangarori na siyasa da ke neman kotun ta hana matakin gwamantin kasar na tura 'yan majalisa zuwa hutu, matakin da ya janyo bacin rai da zanga-zanga a fadin kasar.
Alkalin zai yanke hukunci da safiyar yau Jumma'a
Lauyan da ke wakiltan bangaren gwamnati, Roddy Dunlop QC ya ce batun ba ya karkashin hurumin kotunan kasar.
Wasu 'yan majalisa 75 ne suka shigar da wannnan karar a Scotland domin kotun ta hana Firai minista Boris Johnson rufe majalisa na mako biyar.
'Yan majalisan sun fara daukan wanna matakin ne a Court of Sessions da ke birnin Edinburgh tun a watan jiya.
Amma tuni Sarauniyar Ingila ta amince da bukatar Mista Johnson na rufe majalisar a watan Satumba da Oktoba.
Masu sukan matakin na ganin rufe majalisar zai hana 'yan majalisa samun isasshen lokacin kafa dokokin da za su kare Birtaniya daga fadawa hadarin ficewa daga Tarayyar Turai a ranar 31 ga watan Oktoba ba tare da kulla wata yarjejeniya ba.











