Gboyega Oyetola: APC ce ta lashe zaben Osun – Kotun Koli

Asalin hoton, OfficialAPCNg
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara wanda ya ce Gwamna Adegboyega Oyetola ne ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
A watan Maris ne kotun sauraron kararrakin zabe ta ayyana Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben watan Satumbar shekarar 2018.
Daga nan ne sai Gwamna Oyetola ya daukaka kara.
Shugaba Buhari ya wallafa sakon taya Oyetola murna a shafinsa na Twitter inda ya ce: "Ya zama wajibi na taya Gwamna Gboyega Oyetola na Jihar Osun murna kan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar masa da nasararsa a zaben gwamna da aka yi a watan Satumbar 2018."
Ya kara da cewa: "Wannan hukuncin na Kotun Koli ya kawo karshen turka-turkar da ake yi a kan kujerar gwamnan Jihar Osun, ya kuma kawar da duk wani dabaibayi da ka iya hana gwamnan samar wa al'ummar jihar romon dimokuradiyya."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
A nasa bangaren kuwa Atiku Abubakar dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP a 2019, jaje ya taya Sanata Ademola Adeleke kan abin da ya faru.
"Na shiga sahun dukkan 'yan Najeriya masu kishinta wajen shaida wa Sanata Ademola Adeleke da al'ummar jihar Osun cewa, muna tare da su a lokutan dadi da na wuya.
"Kotun koli ta yanke hukunci kuma da yake daga ita ba sauran daukaka kara, to batun karar ya zo karshe.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Hukuncin kotun kolin na ranar Juma'a ya amince da hukuncin kotun daukaka kara wanda ya jingine hukuncin sauraron kararrakin zabe.
Kotun ta ce alkalin da ya karanta hukuncin a kotun sauraron kararrakin zabe Peter Obiora ba ya nan a ranar 6 ga watan Fabrairun.
Ta ce rashin bayyanar Mista Obiora a ranar yanke hukuncin hakan yana nufin cewa kotun sauraron kararrakin zaben ba ta da hurumin yanke hukuncin.
Sai dai biyu cikin alkalan kotun kolin bakwai ba su amince da wannan hukuncin ba.
Mai Shari'a Bode Rhodes-Vivour ne ya karanta hukuncin kotun kolin.
Dan takarar PDP Mista Adeleke ne ya fara shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zabe inda yake kalubalantar nasarar da Mista Oyetola na APC ya samu a zabukan ranakun 22 da kuma 27 ga watan Satumbar 2018.
Wannan hukunci dai na kotun koli ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar inda wasu ke jinjinawa kotun wasu kuma suke zaginta.












