Duniyar jarida ta rasa Umar Sa'id Tudun Wada

Umar Sa'idu Tudun Wada

Asalin hoton, facebook

Bayanan hoto, Marigayi Umar Tudun Wada ya yi gogayya da jama'a

Alhaji Umar Sa'idu Tudun Wada ya rasu ne sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta koma wa Kano daga Abuja, da yammacin Lahadin nan.

Marigayin ya rasu ya bar mata uku da yara da dama.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Umar ya kasance gogaggen dan jarida wanda ya rike gidan rediyon jihar Kano a baya-bayan nan.

Ya kuma rike shugaban rukunin tashoshin Freedom Radio a jihar ta Kano.

Alhaji Umar ya yi aiki da gidan rediyon VOA a Amurka sannan yana daya daga cikin mutanen da suka bude gidan talbijin mallakar jihar Kano wato CTV a 1981.

Marigayin ya rike kujerar mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai ga tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, a 2011.

Jama'a da dama na ci gaba da aike wa da ta'aziyya ta kafafen watsa labarai da ma na soshiyal midiya.