Trump ya zama shugaban Amurka na farko da ya shiga Koriya ta Arewa

Shugaba Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko wanda ke kan mulki da ya taka kafarsa a kasar Koriya ta Arewa, inda ya bayyana cewa shugaban kasar ne Kim Jong-un ya gayyace shi.

Tun da farko Mista Trump ne ya mika goron gayyata ga takwaran nasa na Koriya ta Arewa ta wani sakon Twitter ranar Asabar, cewa yana gayyatarsa su gaisa a kan iyakar kasashen Koriyar.

Trump ya je Koriya ta Kudu ne inda suka gana da shugaban kasar Moon Jae-in, inda daga nan ne ya je kan iyakar, har ta kai ma ya shiga bangaren iyakar ta makwabciyar mai masaukin nasa.

Wannan ne bulkaguro na farko da Shugaba Trump ya sa kafarsa a kan yankin da ya raba kasashen biyu 'yan uwan juna amma kuma wadanda ke kai ruwa rana a tsakaninsu.

Kuma kamar yadda ziyarar ta dau hankali, haka kuma tambaya daya daman da mutane ke yi ko zuba ido su gani shi ne amsa gayyatar ta Trump da Shugaba Kim Jong-un ya yi.

Hukumomin Koriya ta Arewar sun bayyana goron gayyatar da Shugaba Trump ya mika wa shugaban kasarsu ta sakon twitter, na yin hannu da shugaban, su gaisa a kan iyakar, da cewa abu ne mai kyau.

Amma kuma da farko sun bayyana cewa babu tabbacin cewa ko Mista Kim zai amsa wannan gayyata, domin a hukumance sun ce ba su samu gayyatar ba.

wannan haduwa ta shugabannin ta kasance ta uku kenan a kusan sama da shekara daya, kawai.

Zaman tattaunawarsu na Hanoi a watan fabrairu ya watse bayan da suka kasa warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu a kan bukatun Amurka na kawar makaman nukiliya, da kuma bukatun Koriya ta Arewar na sassauta mata takunkumi.

Mista Trump ya gana da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in kafin ya je kan iyakar, inda kallo ya karkata can, kowa aka zuba ido a ga abin zai wakana; Kim Jong-un zai hallara ko kuwa zai yi burus da gayyatar ta shugaban na Amurka.