An sanya wa ungulaye 500 guba sun mutu a Botswana

A Hooded Vulture waits to get to the scraps of a lion kill

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu kare muhalli sun ce mutuwar ungulayen abu ne maras dadin ji

Fiye da ungulaye 500 da suke fuskantar karewa ne suka mutu a Botswana sakamakon sanya musu guba, a cewar jami'ai.

An samu mushen ungulayen 537 da kuma shaho biyu a arewa maso gabashin kasar, duk da cewa ba a san yaushe abin ya faru ba.

Gwamnati na zargin wasu mafarauta ne da suka kashe wasu giwaye uku suka sanya guba a jikin gawarwakin giwayen.

Masu kare muhalli sun bayyana lamarin da cewa yana daya daga cikin kisa mafi girma da aka yi wa wadannan tsuntsaye da dama ke barazanar karewa.

Gwamnatin ta ce sanya gubar "yana da hadari ga muhalli" ta kuma umarci jama'a da su "guji aikata irin wannan mummunan lamari".

Rahotanni sun ce an gyara wajen da abin ya faru ta hanyar kawar da gubar kuma an dauki samfuri don kai wa dakin gwaji a auna.

Ana iya ganin ungulayen da suka zagaye gawarwakin giwayen daga nesa, don haka mafarauta ke sanya musu guba don kar a gane abin da suka yi, kamar yadda wakilin BBC na Afirka Alastair Leithead ya ce.

Mafi yawan wadannan tsuntsaye dai ungulaye ne masu farin baya, wadanda irinsu yake karewa, kamar yadda kungiyar masu kare muhalli ta duniya International Union for Conservation of Nature ta fada.

Bayanan bidiyo, "We've been seeing carcasses of elephants, some four months old, some less than a week old" reports Alastair Leithead, flying over Botswana

Daga cikin ungulayen da suka mutu din akwai 17 masu fararen kai da 28 masu rufaffen kai, wadanda su ma irinsu ke karewa.

Tsuntsayen sun mutu ne a lokacin da suke yawan haihuwa, wanda hakan ke nufin 'ya'yansu ma abin zai shafe su.

Kerri Wolter, shugaban wata gidauniya ta kare ungulaye ta VulPro ya ce, "Da yake ungulaye ba sa haihuwa akai-akai kuma ba sa girma da wuri, rasa kusan 600 a kasa da mako daya abu ne mara dadin ji".

"Idan haka ya ci gaba da faruwa da su to akwai yiwuwar irinsu ya yi saurin karewa."

A watan da ya gabata ne aka dinga ce-ce-ku-ce a Botswana bayan da gwannati ta dage dokar hana farauta.

Gwamnatin ta kare matakinta da cewa giwayen kasar na karuwa kuma suna lalata wa manoma gonakinsu, sannan kuma giwayen sun kashe mutane da dama a kauyuka.

Botswana ce kasar da ta fi kowacce yawan giwaye, inda take da giwaye 130,000.