Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Omo-Agege ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa
Sanata Omo-Agege na jam'iyyar APC ya lashe zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa, inda ya doke Sanata Ike Ekweremadu na jam'iyyar PDP.
Sanatoci 105 ne suka kada kuri'a a zaben mataimakin shugaba - daya ya kaura ce - yayin da kuri'a daya kuma ta lalace.
Omo-Agege ya samu kuri'u 68 yayin da Sanata Ike Ekweremadu ya samu 37.
Tun da farko an zabi Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa.
Ike Ekweremadu shi ne tsohon mataimakin shugaban majalisar, inda ya shafe shekara 12 a kan mukamin.