Masu zanga-zanga a Sudan sun bijire wa dokar hana fita

Masu zana-zanga

Asalin hoton, AFP

Dubban masu zanga-zanga a Sudan sun bijirewa dokar hana fita da sojojin kasar suka saka inda suka kwana kan tituna.

A ranar Alhamis ne sojojin suka hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir wanda ya shafe kusan shekaru 30 kan karagar mulki.

Amma masu zanga-zangar sun bayyana cewa sojojin da suka yi juyin mulki da su aka dama a gwamantin al-Bashir.

Wannan sabuwar kurar da ta ta so a Sudan na sa jama'a na fargabar yiwuwar fito na fito tsakanin masu zanga-zangar da kuma jami'an tsaro a kasar.

Akwai kuma babbar barazanar da ake ganin cewa jami'an tsaro tsakaninsu na iya juya wa kawunansu baya su yaki juna kamar yadda Editan BBC na Afirka Will Ross ya bayyana.

A yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Tarayyar Afrika sun yi kira da a zauna lafiya.

Me masu zanga-zangar ke cewa?

Har zuwa yanzu, akwai dubban masu zanga-zangar da suka yi zaman dirshen a gaban shelkwatar rundunar sojojin kasar inda suke gudanar da zanga-zangar.

Murnar da aka yi a ranar Alhamis bayan sanarwar da aka yi ta juyin mulki a Sudan ta bar baya da kura sakamakon kiraye-kirayen da manyan kungiyoyi masu gudanar da zanga-zanga a kasar suke yi na a ci gaba da zaman dirshen a gaban shelkwatar sojojin kasar.

Sara Abdeljalil, daya daga cikin 'yan kungiyar da ke jagorantar zanga-zanga a kasar ta bayyana cewa ''wannan ci gaba da tsohon mulkin al-Bashir ne kawai, abinda yakamata mu yi shi ne mu ci gaba da gwagwarmaya.''

Tun a baya kungiyar mai jagorantar zanga-zangar ta bayyana cewa ba za su yadda wani daga cikin wadanda suka gudanar da mulkin kama karya ba ya jagoranci Sudan.