Ana ci gaba da zanga-zanga a Sudan

Asalin hoton, Getty Images
Jama'a sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya sauka daga mulki a daidai lokacin da ake jiran jawabin daga rundunar sojin kasar a ranar Alhamis.
Tun da farko an girke sojoji a ma'aikatar tsaron kasar da tituna da gadoji a birnin Khartoum.
Sai dai har yanzu rundunar sojin ba ta ce uffan ba tukuna.
Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya ruwaito wata majiya tana cewa Shugaba al-Bashir, wanda ya shafe kusan shekara 30 a kan mulki, ya sauka daga mulki kuma an fara shirye-shiryen kafa gwamnatin rikon kwarya.
Ana saran za su fitar da wata sanarwa a nan gaba a gidan talabijin da rediyo yayin da aka shiga rana ta shida a jere da fara zanga-zanga.
Akwai dandazon jama'a a wajen hedkwatar sojoji da ke birnin Khartoum kuma sun sha alwashin cewa ba za su bar wurin ba har sai shugaban kasar ya yi murabus.
Ana sanya wakokin kishin kasar a gidajen rediyon kasar kuma an rufe babban filin jirgin saman kasar.
Wasu sun fara murna a kan titunan kasar a Khartoum kuma suna kira ga sauran jama'a da taru a gaban hedkwatar tsaron kasar.











