Najeriya na sa ido bayan abin da ya faru a Sudan

Labarai da sharhi game da yadda ake rikicin siyasar Sudan, yayin da aka shiga kwana shida a jere na zanga-zangar adawa da Shugaba Omar al-Bashir.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita and Umar Rayyan

  1. Najeriya na sa ido bayan abin da ya faru a Sudan

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana sa ido kan lamarin da ke faruwa a Sudan bayan sojoji sun hambarar da Gwamnatin Omar al-Bashir.

    Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaida cewa abinda Najeriya ta damu da shi, shi ne kada a yi rikici kuma a dawo da mulkin dimokradiya ba da dadewa ba.

    Ministan ya shiadawa BBC cewa ''har yanzu muna samun labarai kan abinda ke faruwa duk da cewa ba mu da cikakkun bayanai da alkaluma amma abinda muke so a bayyane yake; abu na farko shi ne kada a yi rikici.''

  2. Me zai biyo baya?

    Wannan wani juyin mulki ne da babu cikakken bayani kan yadda manyan sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Sudan za su mika mulki ga farar hula.

    Jami'an tsaro a kasar tuni suka lissafa cewa hambarar da al-Bashir da kuma saka dokar hana fita zai samar masu lokaci kuma a kawo karshen zanga-zangar.

    Idan wannan maganar hakane, akwai rashin lissafi a wannan lamari domin kuwa kungiyar da ke jagorantar zanga-zanga a Sudan wato Sudanese Professionals Association da sauran kungiyoyi masu zaman kansu tuni suka bayyana cewa baza su yadda da wannan jawabin da shugaban sojojin kasar ya yi ba.

    Kungiyoyin suna da dumbin magoya baya kuma a shirye suke, haka kuma su ma sojoji a kasar suna da bindigogi da kuma karfin take duk wanda ya tayar da tarzoma.

  3. Ina Omar al-Bashir?

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ne Janar Auf ya sanar da cewa za a kama Shugaba Omar al-Bashir a kai shi wani kebaben wuri.

    Amma a halin yanzu ba a san inda yake ba.

    Rahotan karshe da kafafen yada labarai na kasar suka yi kan shugaban shi ne a lokacin da ya hallarci wani taro a kasar a ranar Litinin.

    Rashin bayyanar shugaban a fili ne ya kawo cece-kucen da ake yi na ina shugaban ya shiga?

    Kafar yada labarai ta CNN ta ruwaito cewa yana tsare ne a gida amma kafar BBC har yanzu ba ta tabbatar da haka ba.

  4. Na hudu a dadewa a jerin masu mulki a yanzu

    Kafin a hambarrar da gwamnatin Omar al-Bashi, shi ne na hudu a dadewa kan mulki a jerin masu mulki a halin yanzu.

    BBC
  5. Hotunan yadda wasu ke murna a Sudan

    Ahmad Muhammad Karika

    Asalin hoton, Ahmad Muhammad Karika

    Ahmad Muhammad Karika

    Asalin hoton, Ahmad Muhammad Karika

    Ahmad Muhammad Karika

    Asalin hoton, Ahmad Muhammad Karika

  6. Kun san wanda ya karanta jawabin juyin mulki a talabijin?

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Ministan tsaron Sudan kuma mataimakin shugaban kasar Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf ne ya karanta jawabin juyin mulkin kasar.

    Laftanar Janar Auf mai shekaru 65 a lokacin wa'adinsa a matsayin ministan tsaron kasar, ya kawo ci gaba ta fannin kayan yaki a kasar.

    Ya taba zama shugaban bangaren tattara bayanan sirri na sojojin kasar.

    Kwarewarsa a matsayinsa na soja da kuma kwarewar siyasa ta sa ya zama wanda ake tunanin zai maye gurbin Mista Bashir ko kuma ya taka rawa wajen wanda zai gaji shugaban.

    Yana daga cikin wadanda Amurka ta saka sakawa takunkumi bayan rikicin kabilancin da aka yi a Darfur.

    Amurka ta zarge shi a matsayin mai shiga tsakani da gwamnatin kasar da kuma 'yan tada kayar baya na Janjaweed.

    A wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a 2005, binciken ya saka Ibn Auf a jerin sunayen wadanda suka sa rikicin Darfur ya kazanta wanda hakan ya sa Amurka ta toshe kadarorinsa tun 2007.

  7. Labarai da dumi-dumi, Kungiyar da ke jagorantar zanga-zanga a Sudan ta yi watsi da jawabin Sojoji

    Kungiyar da ke jagorantar zanga-zangar hambarar da gwamnatin al-Bashir ta yi watsi da jawabin da ministan tsaron kasar ya yi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato kungiyar Sudanese Professionals Association na cewa.

    Kungiyar ta yi kira ga masu zanga-zangar da su ci gaba da zama wajen rundunar sojojin kasar da ke birnin Khartoum.

  8. Kadan daga jawabin juyin mulkin Sudan

    BBC

    Kadan daga cikin abubuwan da Sojoji suka bayyana a jawabinsu na hambarar da gwamnatin al-Bashir.

    • Za a kama Omar al-Bashir a kai shi kebaben wuri da za a kula dashi
    • Za a sa dokar ta baci a kasar na tsawon wata uku
    • Sojoji za su kula da kasar a lokacin wa'adin da aka kebe na shirye-shiryen mika mulki
    • Za a kafa wani kwamiti na sojoji da za su kula da shirye-shiryen mika mulki
    • Za a soke amfani da kundin tsarin mulki na 2005.

    Bugu da kari, ministan tsaron kasar Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf ya bayyana cewa za a lura da hakkin dan adam kuma ya bukaci 'yan kasar da su yi hakuri da matakan da sojoji za su dauka a kasar.

  9. Rayuwar Omar al-Bashir a takaice

    Al-Bashir

    Asalin hoton, Getty Images

    • An haife shi ne a shekarar 1944
    • Tsohon sojan ya hau mulki ne a shekarar 1989 ta hanyar juyin mulki
    • Ya karbi mulki ne a lokacin da kasar take tsakiyarr yakin basasa tsawon shekara 21, tsakanin arewaci da kudancin kasar
    • An kawo karshen yakin ne a shekarar 2005
    • Sabon yaki ya sake barkewa a shekarar 2005 a yankin Darfur
    • Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) tana nemansa ruwa-a-jallo saboda zargin kisan kiyashi a yakin Darfur.
    • Ya lashe zabe a 2010 da kuma 2015
    • An yi kwana shida a jere ana zanga-zangar adawa da al-Bashir.
  10. Labarai da dumi-dumi, Sojoji sun kama al-Bashir

    Bayan shekaru 30 kan karagar mulki, Sojoji sun hambarar da gwamnatin Shugaban Sudan Omar al-Bashir kamar yadda ministan tsaro na kasar ya bayyana.

    Wannan na zuwa ne bayan doguwar zanga-zanga da kuma matsin lamba da shugaban ya samu daga 'yan kasar.

  11. Tarihi: Rawar da sojoji suka taka a siyasar Sudan

    Rundunar sojojin Sudan ta taka muhimmiyar rawa wajen siyasar kasar tun bayan samun 'yancin kai a 1956.

    An soki sojojin kasar bisa yin amfani da fushin da mutane suke ciki domin ya zama hujja na hawa kan karagar mulki.

    • A 1958 shekaru biyu bayan samun 'yancin kan kasar, Shugaban Sojojin Kasar Janar Ibrahim Abboud ya karbi mulki bayan wani juyin mulki da aka zubar da jini.
    • Matsin lamba yasa sojojin suka mika mulki a 1964.
    • A 1969, Kanal Jaafar el-Nimeiri ya yi juyin mulki inda shi ma ya tsallake kokarin hambarar da shi.
    • Amma a 1985, Janar Abdel Rahman Swar al-Dhab ya jagoranci juyin mulkin da aka hambarar da el-Nimeiri.
    • Bayan shekara daya, al-Dhahab ya mika mulki ga zababbiyar gwamnatin dimokradiya ta Sadiq al-Mahdi.
    • Amma bayan shekaru uku, a watan Yunin 1989, sojojin kasar karkashin jagorancin Janar Omar al-Bashir suka hambarar da gwamnatin al-Mahdi.

    Bayan shekaru 30, Bashir ya ci gaba da zama shugaban kasar bayan ya fuskanci kalubale daban-daban a mulkinsa.

    A halin yanzu, 'yan kasar na dakon jin shugaban kasar ya fito ya bayyana saukarsa daga kan karagar mulkin.

  12. Sudan ta dau zafi

    Akwai daya daga cikin masu zanga-zanga da ke wajen shelkwatar rundunar sojojin Sudan da ya aiko wa BBC da sako inda yake bayyana cewa ''kasar ta dau zafi a daidai lokacin da ake jiran jin jawabin shugaban ta rediyo.''

    Masu zanga-zangar na jiran jawabin da sojojin kasar suka yi masu alkawarin cewa za a yi kusan sa'o'i bakwai da suka wuce amma gidajen rediyon kasar na saka wakokin sojoji ne kawai.

    Akwai jita-jitar da ake yadawa cewa sojojin za su tursasawa Shugaba al-Bashir ya sauka.

  13. Wane ne Omar al-Bashir

    Omar al-Bashir

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Sudan, Omar Al Bashir ya fara mulkin kasar tun a 1989.

    Ya fafata a yaki da Isra’ila, kuma ya jagoranci zanga-zanga ga masu kiran a dakile yan tada kayar baya da ke yankin Darfur da kuma kudancin Sudan.

    Shugaban, shahararren dan siyasa ne wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC ta zarga da aikata wasu laifukka.

  14. Shin da gaske ne al-Bashir ya sauka daga mulki?

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Jama'a sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya sauka daga mulki a daidai lokacin da ake jiran jawabin daga rundunar sojin kasar a ranar Alhamis.

    Tun da farko an girke sojoji a ma'aikatar tsaron kasar da tituna da gadoji a birnin Khartoum.

    Sai dai har yanzu rundunar sojin ba ta ce uffan ba tukuna.

    Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya ruwaito wata majiya tana cewa Shugaba al-Bashir, wanda ya shafe kusan shekara 30 a kan mulki, ya sauka daga mulki kuma an fara shirye-shiryen kafa gwamnatin rikon kwarya.

    Ana saran za su fitar da wata sanarwa a nan gaba a gidan talabijin da rediyo yayin da aka shiga rana ta shida a jere da fara zanga-zanga.

    Akwai dandazon jama'a a wajen hedkwatar sojoji da ke birnin Khartoum kuma sun sha alwashin cewa ba za su bar wurin ba har sai shugaban kasar ya yi murabus.

    Ana sanya wakokin kishin kasar a gidajen rediyon kasar kuma an rufe babban filin jirgin saman kasar.

    Wasu sun fara murna a kan titunan kasar a Khartoum kuma suna kira ga sauran jama'a da taru a gaban hedkwatar tsaron kasar.

  15. Me yasa ake takaddama da Shugaban Sudan?

    Ana sukar mulkin Mista Bashir da take hakkin bil adama.

    Ana ganin cewa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na da yiwuwar bayar da takardar sammaci a gareshi sakamakon zarge-zargen da ake yi masa na kisan kiyashi da kuma laifuffuka da suka shafi yaki da kuma laifin take hakkin bil adama.

    Amurka ta saka wa kasar takunkumi shekaru 20 da suka gabata inda Amurkar ke zargin Khartoum da daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda.

    A bara, darajar kudin Sudan ya fadi warwas wanda hakan ya yi sanadiyar samun tashin gwauron zabin kayayyaki.

    A watan Fabrairu, an yi zaton shugaban zai yi murabus, amma sai aka ji kwatsam shugaban ya sa dokar ko ta kwana.

  16. Hotunan masu zanga-zanga

    An ci gaba da zanga-zanga a titunan birnin Khartoum, yayin da ake ci gaba jiran sanarwa daga rundunar sojin kasar Sudan.

    Sudan

    Asalin hoton, Reuters

    Sudan

    Asalin hoton, APF

    Sudan

    Asalin hoton, Reuters

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Sudan

    Asalin hoton, Reuters

  17. Kun san irin tasirin mata a zanga-zangar Sudan?

    Kiyasi ya nuna cewa mata su ne kashi biyu bisa uku na yawan wadanda suka ringa halartar zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shugaba Omar Al-Bashir.

    Bayanan bidiyo, Kun san tasirin mata a zanga-zangar Sudan?
  18. Jama'a barka da war haka!

    Jama'a barka da shigowa wannan shafi wanda za mu rika kawo maku labarai da bayanai kan halin da ake ciki a kasar Sudan, yayin da aka shiga kwana shida a jere na zanga-zangar adawa da Shugaba Omar al-Bashir.