Trump na so a yi shari'ar mayakan IS

Shugaban Amurka Donald Trump ya gaya wa Birtaniya da sauran kawayensu na Turai su karbi mayakan kungiyar da ke ikirarin kishin Musulunci ta Islamic State, IS, kimanin 800 wadanda aka kama a fagen daga sannan su yi musu shari'a.

Ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a Twitter a yayin da kungiyar Kurdawa da Amurka ke mara wa baya take ci gaba da kai hari kan gyauron mayakan IS a kan iyakar Syria da Iraki.

Dakarun Kurdawa ne dai ke tsare da mayakan na IS.

Mr Trump ya kara da cewa daular da mayakan ke fafutukar kafawa "ta kusa rushewa."

"Amurka ba ta so wadannan mayaka na IS su mamaye Turai, inda ake sa ran za su je. Muna yin aiki tukuru sannan muna kashe kudi mai yawa - Yanzu lokaci ne na wasu kasashe za su tashi tsaye su yi aikin da ya kamata", in ji shi a sakon Twitter.

Ya ce idan ba haka ba, Amurka za ta saki mayakan na IS.

Wasu jami'an gwamnatin Trump sun shaida wa jaridar Sunday Telegraph cewa suna tsoron cewa wasu daga cikin mayakan IS ka iya zama barazana ga Turai idan ba a yi musu shari'a ba.

Wadannan kalamai na Donald Trump sun yi daidai da wadanda wani jami'in ma'aikatar wajen Birtaniya ya yi ranar Juma'a, inda ya yi gargadin cewa mayakan IS na sake taruwa domin kaddamar da manyan hare-hare duk da murkushewar da aka yi musu a Syria.