Taskun da 'yan Najeriya suka shiga bayan dage zaben INEC

Asalin hoton, AFP
'Yan Najeriya da dama sun wayi gari suna tunanin ko labarin dage zabe a kasar labarin kanzon kurege ne.
A tsakar dare ne sa'o'i biyar kafin bude rumfuna don gudanar da babban zabe a kasar, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriyar Mahmood Yakubu ya bayyana wa wani taron manema labarai da aka shirya cikin gaggawa cewa an dage zaben da mako daya saboda matsalar da aka samu wajen kai kayayyakin zaben.
Bayan haka ne wasu daga cikin 'yan kasar suka nuna rashin jin dadinsu da baccin ransu.
Musa Abubakar wanda ya shafe tafiya mai tsawo tun daga birnin tarayyar Najeriyar zuwa garin Daura da ke jihar Katsina kimanin tafiyar kiolomta 550 ya bayyana wa BBC cewa ya kasa amincewa da wannan lamari saboda mamaki.

Yana daga cikin 'yan kasar da suka yi tattaki zuwa garuruwansu domin kada kuri'a.
''Ban san abinda zan yi ba, ban ji dadi ba," in ji Abubakar.
A halin yanzu yana da zabin tsayawa Daura amma ba zai samu zuwa wajen aikinsa ba ko kuma zabin kara tafiya daga Abuja zuwa Daura ko kuma ka da ya yi zaben gaba daya.
Nuna takaici a shafin intanet
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wani mai amfani da shafin Twitter kenan yake cewa ''mutane sun shiga motoci sun yi tafiya sakamakon wannan zaben amma an dage shi a safiyar da ya kamata a gudanar da shi.

Wasu kuma na yada wani bidiyo da shugaban hukumar zaben a wata hira da ya yi a kwanakin baya inda ya bayyana cewa ''babu alamun dage wannan zabe,'' inda mutane suke mamakin yadda ya saba wadannan kalamai nasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shin dage zaben zai iya kawo matsala dangane da fitowar mutane a ranar zabe?
Wadanda suke da niyyar jefa kuri'a sun dade suna shirin yin hakan.
Kafin dage zaben, an yi niyyar takaita zirga-zirga a kasar wanda hakan zai sa mutane ba su da wani zabi illa su jefa kuri'a ko kuma su zauna a gida.
Hajiya Sa'adatu ta bayyana rashin jin dadinta a daidai lokacin da ta fito domin kada kuri'arta a arewacin birnin Kano inda ta samu labarin cewar an dage zaben.

Akwai damuwa dangane da dage wannan zaben inda ake tunanin cewa mutane kalilan ne za su fito mako mai zuwa domin kada kuri'arsu.
A kudancin birnin Owerri, Chukwueze (ya bayyana wa BBC sunanshi na farko ne kawai) ya bayyana bacin ransa. inda ya ce ''Najeriya ta nuna cewa cin hanci ya yi mata katutu,'' ya kuma ce ''mako mai zuwa ba za mu fito ba.''
Amma duk da haka guiwar wasu ba ta sanyaya ba.
Abubakar Shettima da ke jihar Filato a Najeriyar ya fara bin layin zabe ne tun a ranar Alhamis inda ya shaida wa BBC cewa yana so ya zama mutum na farko da zai fara kada kuri'arsa.
A lokacin da yake mayar da martani a kan dage zaben ya shaida cewa har yanzu yana da yakinin dawowa.
A birinin Yolar jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar, Yucehe Ogbu ta shaida cewa za ta yi zabe mako mai zuwa inda ta ce ''idan ka yi zabe za ka iya kawo sauyi.''











