Ba zan zabi Buhari ko Atiku ba - Wole Soyinka

Fitaccen marubucin nan na Najeriya wanda ya taba lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa ba zai goyi bayan Muhammadu Buhari ko Atiku Abubakar ba a zaben kasar da za a gudanar a watan Fabrairun 2019.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yana neman shugabancin kasar inda yake kalubalantar Muhammadu Buhari wanda shi ke shugabantar Najeriya a halin yanzu.
Amma akwai wasu mutane kimanin 70 wadanda suke neman shugabancin Najeriya.
"Dukkaninsu [Buhari da Atiku] ba su cancanci a zabe su ba" a cewar Soyinka.
Ya kara da cewa "Ra'ayina shi ne lokaci ya yi da ya kamata a bi sabuwar hanya".
Farfesa Soyinka ya bayyana cewa 'yan gwagwarmaya suna tattaunawa a kan yadda za su fitar da dan takara daya wanda zai cancanci a zabe shi.
Soyinka ya aminta da cewa zabar wani wanda ba su ba ba lallai bane ya yi tasiri. Amma ya ce hakan "Zai iya fitar da tsoron da zai girma a gaba".








