Abin da ya sa Buhari da Atiku suka ki zuwa muhawara

Buhari da Atiku

Asalin hoton, Getty Images

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce shugaba Buhari ne warin muhawararsa.

A wata sanarwa da ya aike wa BBC dan takarar na PDP ya ce ba zai iya bata lokaci yana kalubalantar gwamnati a bayan idon wanda alhakin tafiyar da kasa ke hannunsa.

Ya ce ya fi son su hadu domin ya kare kansa.

'Yan takarar manyan jam'iyyun guda biyu a Najeriya APC da PDP sun kaurace wa muhawarar ne da aka shirya tsakanin 'yan takara biyar ranar Asabar a Transcorp Hilton.

Hukumar watsa labarai ta Najeriya BON da kuma kungiyar da ke shirya muhawarar zabe NEGD suka shirya muhawarar domin fahimtar manufofin 'yan takarar.

Muhawarar ta kare ne tsakanin 'Yan takara uku da suka hada da Oby Ezekwesili ta ACP da Fela Durotoye na ANN da kuma Kingsley Moghalu na YPP.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa kwamitin yakin neman zaben Buhari ne ya bada shawarar a kauracewa muhawarar

Ya ce sun lura muhawarar ba ta cancanta da shi ba, musamman 'yan takarar da aka zaba da kuma tsarin muhawarar.

Ya ce an rubuta takardar hakuri ga wadanda suka shirya muhawarar.

Dan takarar na ya halarci zauren muhawarar amma daga baya ya kaurace bayan ya ji cewa Buhari ba zai zo ba.

Atiku ya kalubalanci shugaba Buhari ya zabi rana da lokaci domin yin wata muhawarar da zai iya halarta tare da wasu 'yan takarar.

'Yan takara daga jam'iyyu 72 ne ke neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019 a Najeriya.