'An kashe 'yan Boko Haram sama da 280 a Nijar'

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce sojojin kasar sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 280 a hare-haren sama da na kasa da aka kai musu a kan iyakar kasar da Najeriya.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar wacce aka watsa a gidan talbijin din kasar ta ce akasarin mayakan Boko Haram din sun mutu ne sanadin hare-haren da aka kai musu ta sama.

Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta kara da cewa dakarunta sun kuma kama na'urorin harba makamai da harsasai lokacin da suka kai farmaki a maboyar 'yan Boko Haram da ke yankin Tafkin Chadi da kuma kan hanyar Kogin Komadougou Yobe.

A 'yan kwanakin nan Jamhuriyar Nijar ta nuna matukar damuwa kan koma bayan da ake samu a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kwashe kusan shekara goma tana kai hare-hare musamman a makwabciyarta, Najeriya.

Wannan lamari na faruwa ne kwanaki kadan bayan rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta murkushe hare-haren mayakan Boko Haram a garin Baga na jihar Borno.

A washegarin kirsimeti ne mayakan Boko Haram suka shiga garin Baga suka yi musayar wuta da na sojojin Najeriya inda wasu rahotanni suka ce har kwace ikon garin tare da kafa tuta.