Zamfara: Sarki ya ce a ba 'yan kato da gora bindigogi

Sarkin ya ce 'yan kato da gora ba su da wani makamin kare kai da ya wuce sanduna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarkin ya ce 'yan kato da gora ba su da wani makamin kare kai da ya wuce sanduna

Wani basaraken gargajiya a Najeriya ya bukaci gwamnatin kasar ta bai wa 'yan kato da gora kayan aiki, don taimaka wa yaki da gungun masu aikata laifuka a kasar.

Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad ya ce Civilian JTF ko 'yan kato da gora, ba su da wani makamin kare kai da ya wuce sanduna yayin da masu tayar da kayar baya kuma ke amfani da manyan makamai kamar bindigar AK47 da sauransu.

Masu aikata laifin dai sun hada da barayin shanu, da satar mutane don karbar kudin fansa da sauran laifuka irin wannan.

Sarkin ya ce bai wa 'yan kato da gora su 8500 makamai, ita ce sassaukar hanyar shawo kan matsalar da ta ki ci taki cinyewa.

Hare-haren da barayin shanu da masu satar mutane don kudin fansa ke yi a Zamfara na karuwa a baya-bayan nan, duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen ayyukansu.

Ko a ranar Talata me 'yan sandan Najeriya sun ce jami'ansu 16 ne suka mutu a jihar bayan wata arangama da suka yi da barayin shanu a karamar hukumar Birnin Magaji ranar Alhamis din da ta gabata.

Wannan layi ne

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Sharhi kan tarihin rikice-rikice a Zamfara - Daga Kadariyya Ahmed

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.

A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala'i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar 'yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.

Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan 'yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi
Bayanan hoto, Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi

Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.

Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.

A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.

Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

Short presentational grey line

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Wannan layi ne