Firai Ministan Ethiopia ya nada mata rabin ministocinsa

Asalin hoton, AFP
Firai Minista Abiy Ahmed na Ethiopia, ya nada mata rabin ministocin majalisar zartarwarsa, ciki har da ministar tsaro.
Da yake bayani kan matakin nasa ga 'yan majalisar dokoki, Mista Abiy ya ce mata ba su faye "cin hanci da rashawa kamar maza ba" kuma za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A yanzu Ethiopia ce kadai kasar da take da wakilcin jinsi daidai a majalisar zartarwa a Afirka bayan Rwanda.
Haka kuma Mista Abiy ya rage yawan ministocin kasar daga 28 zuwa 20.
Tun bayan zamowarsa Firai Minista a watan Afrilu ya yi manyan sauye-sauye da dama.
Ya kawo karshen rikicin da aka shafe gomman shekaru ana yi tsakanin kasarsa da makwabciyarta Eritrea, ya kuma saki dubban fursunonin siyasa tare da saussauta matsin da ake fama da shi a fannin tattalin arzikin kasar.
Aisha Mohammed ce ta zama ministar tsaron Ethiopia ta farko.
'Yar asalin yankin Afar ne da ke arewa maso gabashin kasar, ta kuma taba yin aiki a matsayin ministar gine-gine.
Muferiat Kamil wadda tsohuwar shugabar majalisar kasar ce ta zama ministar Zaman Lafiya.
Za ta dinga lura da al'amuran da suka shafi leken asirin kasar da tsaro da kuma hukumar 'yan sandan tarayya.
Mahlet Hailu, wanda shi ne matamakin wakilin dindindin na kasar a Majalisar Dinkin Duniya, ya wallafa jerin sunayen sabbin ministocin a shafinsa na Twitter:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Mista Abiy ya ce matakin sauye-sauyensa na bukatar ci gaba da magance matsalolin da suka jefa kasar cikin rudani.
Ya ce mata sun bayar da gagarumar gudunmowa wajen dawo da zaman lafiya, ba su faye cin hanci ba, suna girmama aikinsu kuma za su iya daurewa wajen kawo sauyi.

Asalin hoton, Reuters
A watan Afrilu ne Mista Abiy mai shekara 42 ya zama Firai Minista bayan da Hailemariam Desalegn ya yi murabus din ba zata.
Bayan haka an shafe shekara uku 'yan kabilar Oromo na zanga-zangar abun da suka kira neman hakkinsu kan nuna musu wariya da ake yi ta fuskar siyasa da tattalin arziki.
Shi kansa Mista Abiy dan kabilar Oromo ne, amma burinsa na ganin an samu yarda da hadin kai da yake yi wa lakabi da "warkewar ciwukanmu... da kuma aiki tare don ci gaban kasarmu" bai samu karbuwa ba daga wajen mutane da dama a cikin kasar.

Karanta wasu karin labarai












