Hotunan yadda Saudiyya ta jagoranci sasantawar Eritrea da Ethiopia

Wasu da dama na ganin Saudiyya ta yi abun a yaba mata kan karbar bakuncin taron sasantawar da ta yi, inda ake ganin ba ta faye shigewa gaba don sasanta rikici tsakanin wasu kasashe ba.

Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed da Shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki sun sanya hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya a Saudiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed da Shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki sun sanya hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya a Saudiyya, bayan shafe shekaru suna rikici da juna.
Lokacin taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Eritrea da Ethiopia a gidan sarkin Saudiyya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gudanar da taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ne tsakanin kasashen biyu a Birnin Jiddah, inda Sarki Salman da dansa Yarima Muhammad suka karbi bakuncin taron.
Lokacin da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud yake sa wa shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki sarka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarki Salman ya bai wa shugabannin Ethiopia da Eritrean lambar yabo ta Sarki Abdulaziz Al Saud, wadda ita ce lambar yabo mafi girma ta farar hula ta Saudiyya.
Lokacin da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud yake sa wa Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed sarka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Haka zalika shugabannin biyu sun samu irin wannan lambar yabo daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Shuwagabannin Ethiopia da Eritrea sunyi murna da taimakaon da Sarki Salman yayi wajen ganin sun sanya hannu a wannan yarjejemniyar zaman lafiyar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugabannin Ethiopia da Eritrea sun yi murna da taimakon da Sarki Salman ya yi wajen ganin sun sanya hannu a wannan yarjejeniyar zaman lafiyar.
(Daga hagu) Sakataren majalissar dinkin duniya Antonio Guterres yana magana yayin da Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel Al Jubier yana sauraron shi lokacin taron da kasashen biyu na Ethiopia da Eritrea suka sa hannu a takardar yarjejeniyar zaman lafiya a garin Jeddah.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, (Daga hagu) Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yana magana a wajen taron manema labarai bayan sanya hannun, yayin da Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel Al Jubier, yake sauraron shi lokacin.
(Daga hagu) Shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki, Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud, Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed sun tsaya daukan hoto bayan sun sa hannu yarjejeniuyar zaman lafiya garin Jeddah.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rahotanni sun ce babu tabbas kan irin rawar da Saudiyya ta taka a yarjejeniyar zaman lafiyar, wacce aka cimma watanni biyu da suka gabata.
(Daga hagu) Shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki tare da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai dai duk da haka wasu masana na jinjinawa Saudiyya kan wannan "rawar gani" na karbar bakuncin taron, wani abu da suke cewa ba a saba ganin Saudiyyan ta shige gaba wajen sasanta wani rikici tsakanin wasu kasashe ba.
(Daga hagu) Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed tare da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun bayan nada shi Yarima mai jiran gadon mulkin Saudiyya dai, Muhammad Bn Salman na ta kawo sauye-sauye a kasar, inda 7yake shan yabo da suka.