Rashin lafiyar tabin hankali na karuwa a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Masana kiwon lafiya sun bayyana damuwa kan yadda ba a damu da diba hanyoyin magance matsalar da biliyoyin al'umma ke fuskanta ba da ta shafi tabin hankali da dangoginsu ba
Rahoton mujallar kiwon lafiya ta Lancet da aka wallafa ya zo daidai ne da ranar da aka ware domin matsalar tabin hankali a duniya.
Rahoton ya ce karuwar rashin lafiyar da ta shafi tabin hankali kusan ta shafi kowace kasa a duniya.
Binciken masanan ya bayyana damuwa ga gazawar gwamnatoci na magance talauci da daidaito da rashin bunkasar tattalin arziki a matsayin matsalolin da ke haddasa tabin hankali.
Mujallar ta yi jan hankali kan yadda matsalar ta fara yin kamari tsakanin matasa.
Kuma rahoton ya ce za a yi hasarar dala tirliyan goma sha shida a tattalin arzikin duniya idan ba a magance matsalar ba zuwa 2030.
Ko da yake rahoton bai fayyace tasirin da matsalar za ta yi wa tattalin arzikin duniya ba na hasarar makudan kudaden zuwa 2030. Amma an bayyana cewa matsalar za ta kara cutar da al'umma da kuma tattalin arziki a duniya.
Jagoran binciken masanan Vikram Patel na jami'ar Havard a Amurka ya ce tun shekaru 25 matsalar ke kara girma saboda karuwar jama'a kuma babu wata kasa da ta tashi tsaye domin magance matsalar.
Ya ce babu irin ciwon da ba a damu da ba kyakkyawar kulawa ba irin matsalar rashin lafiyar da ta shafi tabin hankali.
Rahoton ya yi kiran a kawo karshen yawaitar cin zarafin masu fama da lalurar tabin hankali a wasu kasashe, ciki har da azabtar da su da sunan yin magani, da daure su a gidajen kaso da sauransu.











