Abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da wasu 'yan Afirka a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

Bikin Ireecha
Bayanan hoto, 'Yan kabilar Oromo na kasar Habasha sun yi bikin Irreecha a ranar Lahadi. Sun yi kwalliya da tufafin gargajiya, mutane na dibar ciyawa zuwa tafkin Harsadi don nuna godiya ga Allah a farkon bazara.
Wasu matasa sun zabi wannan ranar don daura aure
Bayanan hoto, Wasu matasa sun zabi wannan ranar ta zama ranar daurin aurensu. Angon ya ce yana murnar yin bikinsa a gaban duka mutanen da su ka fito bikin Irreecha.
Magoya baya na murna a wata zanga-zangar adawa inda manyan 'yan takarar shugabancin' yan adawa za su yi magana da magoya bayansu watanni uku kafin zaben da za a gudanar a ranar 29 ga Satumba, 2018 a birnin Kinshasa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya baya na murna a wata zanga-zangar adawa inda manyan 'yan takarar shugabancin kasar za su yi jawabi a gaban magoya bayansu, watanni uku kafin zaben da za a gudanar a ranar 29 ga Satumba, 2018 a birnin Kinshasa.
Masu tallar kayan kawa suna shiryawa a bayan fage kafin su fito su yi tallar kayan a kasar Addis Ababa a makon tallar kayan kawa a ranar 3 ga watan Oktoba, 2018.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu tallar kayan kawa suna shiryawa a bayan fage kafin su fito su yi tallar kayan a kasar Addis Ababa a makon tallar kayan kawa , ranar 3 ga watan Oktoba shekarar 2018.
Ranar Alhamis, ma'aikata a wata masana'anta a Tunisiya su na warewa tare da busar da barkono wanda za a yi amfani da shi wajen sarrafa yajin Harissa, a ranar 3 ga watan October 2018.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Alhamis, ma'aikata a wata masana'anta a Tunisiya su na warewa tare da busar da barkono wanda za a yi amfani da shi wajen sarrafa yajin Harissa, a ranar 3 ga watan Oktobar 2018.
Mata na dauke da lemu da ruwan sayarwa a kan kawunansu su na kallon ayarin motocin 'yan jaridar da ke harhada labarin ziyarar matar shugaban Amurka MelaniaTrump a Accra, Ghana ranar 2 ga watan Oktoba, 2018.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mata na dauke da lemu da ruwan sayarwa a kan kawunansu su na kallon ayarin motocin 'yan jaridar da ke harhada labarin ziyarar matar shugaban Amurka MelaniaTrump a Accra, Ghana ranar 2 ga watan Oktoba, 2018.
'Yan kasar Malawi na rike da tutoci yayin da matar shugaban Amurka Melania Trump ta isa Lilongwe a kasar Malawi a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba, 2018.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan kasar Malawi na rike da tutoci yayin da matar shugaban Amurka Melania Trump ta isa Lilongwe a kasar Malawi a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba, 2018.
Yara a babban birnin Kenya, Nairobi, suna nishadantarwa ta hanyar wasan kwaikwayon Tinga Tinga a ranar Jumma'a, 28 ga watan Satumba, 2018.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yara a babban birnin Kenya, Nairobi, suna nishadantarwa ta hanyar wasan kwaikwayon Tinga Tinga a ranar Jumma'a, 28 ga watan Satumba, 2018.
A rana guda a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu, masu rawar Ballet na shirin yin rawar ran 4 ga watan Oktoba, 2018

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A rana guda a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu, masu rawar Ballet na shirin yin rawar ran 4 ga watan Oktoba, 2018
Dan macukule sanye da kaya masu siffar giwa na nishadantar da magoya bayan kwallon kafa a rufaffen filin wasan kwallon na Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a Abidjan, babban birnin Ivory Coast.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Dan macukule sanye da kaya masu siffar giwa na nishadantar da magoya bayan kwallon kafa a rufaffen filin wasan kwallon na Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a Abidjan, babban birnin Ivory Coast.
A ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba, 2018 an kona tarin hauren giwa a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo a wani yunkuri na hana kashe giwa ba a bisa ka'ida ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba, 2018 an kona tarin hauren giwa a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo a wani yunkuri na hana kashe giwa ba a bisa ka'ida ba.

Hadin mallakar hotuna AFP, EPA, Reuters and Getty Images.