Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kwankwaso ya kaddamar da takarararsa a zaben 2019
Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da takarar neman shugabancin Najeriya a babban zaben shekarar 2019.
Dan siyasar ya kaddamar da aniyyar hakan ne a wani filin taro da ke unguwar Jabi a Abuja ranar Laraba.
Sai dai gabanin hakan, a ranar Talata wani jigo a kwamitin yakin neman zaben Sanata Kwanwaso, Kwamred Aminu Abdussalam, ya yi ikirarin cewa hukumomi sun hana tsohon gwamnan jihar Kano din taron siyasa a wurare biyu a Abuja.
Dubban magoya bayan dan siyasar ne suka taru a dandalin da ya bayyana aniyyarsa ta neman tsayawa takarar.
Kwankwaso na cikin mutane da dama da ke son PDP ta tatsayar da su takara domin fafatawa da Buhari a 2019.
Ba wannan ne karon farko dan tsohon gwamnan yake neman shugabancin kasar ba.
Ya fara neman takarar ne a zaben 2015, sai dai ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari bayan zaben fidda gwani na jam'iyyar APC.
A cikin watan Yuli ne Sanata Kwankwaso da shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki da wadansu gwamnoni da 'yan majalisa da dama suka bar APC zuwa PDP.