Cutar kwalara ta barke a Iraki

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam a Iraki ta ce dubban mutane ne su ka kamu da cuta bayan da su ka sha gurbataccen ruwa a lardin Basra da ke kudancin kasar.
Hukumar sa ido a kan kare hakkokin bil adama a Iraki ta ce likitoci a yankin sun bai wa mutane da dama da ke fama da amai da gudawa kulawa.
Ma'aikatar muhalli ta kasar ta yi kira ga hukumomi a Basra da su gaggauta neman mafita a abunda ta ce matsala ce mai girma.
Rashin wadataccen ruwan sha da wutar lantarki sun kasance manyan batutuwan da su ka haifar da zanga-zanga a Basra da kudancin Iraki a watannin da su ka gabata.







