Rashin tsaro na sa mutane kwana kan bishiya a Zamfara — Amnesty

Zamfara

Asalin hoton, ABDULRAZAK BELLO KAURA

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty Inaternational ta ce mutane a wasu kauyukan da ke fama da hare-haren 'yan fashi suna kwana a kan bishiyoyi ne domin gujewa wa hare-hare.

A hirarsa da, mai magana da yawun kungiyar, Isa Sanusi, ya ce girman matsalar da mutane suke fuskanta a jihar Zamfara ta wuce misali.

Hare-haren da 'yan fashi ke kai wa kauyukan jihar sun rika jan hankalin 'yan Najeriaya yayin da mutane ke kauracewa daga kauyukansu domin neman tsira.

Malam Sanusi ya kara da cewa mutanen kauyukan kamar Kauyen Birane, ba su da nisa da inda barayin suke, "Kuma mutanen suna zaune ne cikin fargaba, ba tare da sanin ko za su kai gobe ba ko kuma a'a."

Ya kara da cewa, da tawagar kungiyar ta je wani kauye da ake kira Gidan Goga, sun tarar da matasa masu yawa wadanda aka harba a "kafa kuma kafafunsu sun fara rubewa."

"Mutanen garin sun daina zuwa gona saboda tsoron 'yan fashin da ke garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

A cikin 'yan makonni biyun nan an kashe mutum fiye da 150," in ji kakakin Amnesty.

zamfara taswira

Mai magana da yawun Amnesty din dai ya ce mutanen yankin suna bukatar taimakon gaggawa ta yadda za su iya samun zaman lafiya tare da komawa gonakinsu.

Gwamnatin Najeriya dai ta yi shelar tura sojoji dubu daya yankin domin dakile matsalar maharan.

Sai dai kuma masharhanta na cewa ba yanzu aka fara tura jami'an tsaro yankin ba.

Wannan layi ne

Adadin yawan mutanen da ke gudun hijira dai na ci gaba da karuwa a jihar Zamfara sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka addabi kauyukan jihar.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce a kalla mutum 18,000 ne suka kauracewa muhallansu sakamakon sabbin hare-haren 'yan bindiga.

ko a ranar Lahadi mai magana da yawun gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya shaidawa BBC cewa kauyuka kusan 20 ne jama'arsu suka yi kaura a karamar hukumar Zurmi kadai.

Ya ce mutanen sun watse a kauyukan na mazabu uku wato Mashema da Birane da kuma kwashabawa a karamar hukumar mulki ta Zurmi.

Mutanen kauyukan suna yin kaura ne zuwa cikin garin Zurmi, wasunsu suna asibitin MDG, wasu kuma suna rayuwa ne a makarantun boko na firamare.

Kuma ana gudun hijira ne sakamakon wasikun barazana da 'yan fashi ke aika wa mutanen kauyukan na Zamfara.

Wannan layi ne
  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu