'Yan bindiga na tayar da garuruwa a Zamfara

zamfara taswira

Adadin yawan mutanen da ke gudun hijira na ci gaba da karuwa a jihar Zamfara sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka addabi kauyukan jihar.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce a kalla mutum 18,000 ne suka kauracewa muhallansu sakamakon sabbin hare-haren 'yan bindiga.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya shaidawa BBC cewa kauyuka kusan 20 ne jama'arsu suka yi kaura a karamar hukumar Zurmi kadai.

Ya ce mutanen sun watse a kauyukan na mazabu uku wato Mashema da Birane da kuma kwashabawa a karamar hukumar mulki ta Zurmi.

Mutanen kauyukan suna yin kaura ne zuwa cikin garin Zurmi, wasunsu suna asibitin MDG, wasu kuma suna rayuwa ne a makarantun boko na firamare.

Kuma ana gudun hijira ne sakamakon wasikun barazana da 'yan fashi ke aika wa mutanen kauyukan na Zamfara.

A makon jiya, mutane da dama aka kashe tare da kone gidaje a hare-haren na 'yan bindiga. Kuma mutane na gudun hijira ne don guje wa hare-haren da kuma garkuwa da su.

Al'amarin, a cewar wasu mazauna kauyukan jihar ya kai har da rana tsaka 'yan bindiga na iya zuwa su sungumi mutum zuwa daji har sai an biya kudin fansa.

An dai kashe daruruwan mutane a Zamfara a tsawon shekara shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar

Jama'ar yankin na sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdul'aziz Yari da gazawa wajen shawo kan matsalar.

Sai dai gwamnatin ta nace cewa tana yin iya kokarinta domin ganin ta kawo karshen lamarin, wanda ya fara haurawa zuwa makwabtan jihohi irinsu Sokoto.

Zamfara

Asalin hoton, Getty Images