Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana fara kada kuri'a Pakistan
An bude rumfunan zabe a Pakistan bayan wani yakin neman zabe mai cike da rikici da kuma zargin katsalandan daga sojojin kasar ciki da harkar zabuka.
Fiye da mutum miliyan 105 ne suka yi rijistar zabe, inda za su zabi wakilan majalisar dokokin kasar.
Masu kada kuri'a za su yi zabe ne daga cikin sama da 'yan takara dubu 3500 da ke neman mukamai dubu 272 a majalisar dokokin kasar.
Ana sa ran yin karon-batta tsakanin jam'iyyar PLMN da ke rike da mulki a tsawon shekara 5 da ta wuce, da kuma jam'iyyar PTI, karkashin jagorancin tsohon dan wasan kurket Imran Khan.
Masu adawa da Khan na cewa sojoji na kokarin ganin sun kawo shi ne kan karagar mulki, sai dai ya musanta hakan.
Tuni dai hukumar kare hakkin dan adam a kasar ta ce akwai yi wuwar gagarumin yunkuri na murde zaben.
Dubban jami'an tsaro aka girke a rumfunan zaben domin tabbatar da tsaro a rumfunan zaben wadanda aka bude tun da misalin karfe takwas na safe agogon kasar wato uku na safe agogon GMT ke nan.
Kasar pakistan dai takasance sojojin kasar na mulki akai-akai a cikin shekara 70.
Wannan zaben na da matukar muhimmanci ga kasar da ma al'ummarta, saboda zai kasance karo na biyu a jere da gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga wata gwamnatin farar hular bayan kare cikakken wa'adin mulki.
An dai daure tsohon prime ministan kasar Nawaz Sharif a farkon wannan wata, bayan da kotu ta kama shi da laifin rashawa.