Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nawaz Sharif zai koma Pakistan duk da za a kama shi
Korarren Firayi ministan Pakistan Nawaz Sharif na kan hanyar komawa gida duk da ya san za a kama shi ne da ya isa kasar.
Mista Sharif na fuskantar daurin shekara 10 a kurkuku saboda laifukan cin hanci da rashawa.
'Yar Mista Sharif din Maryam Sharif ma na fuskantar dauri da zarar sun isa Lahore daga Landan a yau Juma'a.
Ya ce "Duk da cewa na san babu makawa sai an daure ni, amma ba zan fasa komawa Pakistan ba."
A wancan karon da aka taba yanke ma Nawaz Sharif hukuncin dauri a kurkuku, ya zabi ya bar kasar bayan da Saudiyya ta shiga tsakani.
Wannan lamarin ya auku ne a shekarar 1999 bayan da sojin Pakistan suka hambarar da gwamnati mai ci a lokacin.
Amma a wannan karon, ya zabi ya tafi kurkuku duk da cewa yana kasar Ingila ne a halin yanzu.
A wancan zamanin, an dauka cewa ba zai iya jure ma zaman gidan kaso ba ne saboda shagwababbe ne dan wani attajiri.
Amma da alama matakan da yake dauka yanzu sun tabbatar da cewa a shirye yake ya fuskanci dukkan gwagwarmayar da siyasar kasar ta zaba masa.
Kana Sharif ya san cewa za a sami tirjiyar siyasa bayan babban zaben da ke tafe, lamarin da magoya bayansa ke kallo a matsayin wata makarkashiyar siyasa domin kayar da jam'iyyarsa ta PML-N a zaben.
Ya kuma sani sarai cewa wannan matakin na tattare da mummunan tasiri a gre shi, domin zai tafi ya bar matarsa Khulsoom a asibiti, inda ta ke jinyar cutar daji, kuma likitoci na ganin ba ta da sauran lokaci mai yawa kafin rai yayi halinsa.