Hamshakin attajirin Najeriya ya shiga bas da talakawa

Lokacin karatu: Minti 1

Ana yada bidiyon attajirin dan kasuwan Nigeriya, Femi Otedola, a shafukan sada zumunta bayan ya shiga motar bas tare da talakawa a jihar Legas.

A cikin bidiyon da aka wallafa a shafin Instagram na Mista Otedola a ranar Laraba, an gano biloniyan tare da fasinjoji a cikin wani tsohon bas wanda ake kira "Molue".

Yana tafiya ne daga unguwar Sango zuwa Agege a birnin kasuwancin na Najeriya, Legas, bisa ga bayanin da aka wallafa tare da bidiyon.

Babu wani fasinja da ya gane biliyoniyan har sai bayan da ya sauko daga motar.

Bidiyon da aka wallafa a shafin Instagram na Mista Otedola bai bayyana dalilin da ya sa ya hau bas din ba, amma mutane da yawa sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon a kan shafin Twitter: