Matasa na barin addinin Musulunci a Turkiyya

Malama mai kalabi a cikin aji
Bayanan hoto, Wata malama mai kalabi a cikin aji

"Wannan shi kadai ne abinda ya rage a alakar da ke tsakanina da musulunci," a cewar Merve, wadda ta nuna min kallabinta mai launi ja.

Merve na koyar da da darasin addini ga yara a wata makarantar firamare da ke Turkiyya. A baya mai tsatsauran ra'ayin Islama ce .

"In ban da a baya-bayan nan ba na musabaha da maza," ta fada mani haka a wani kantin shan shayi da ke Istanbul. "Amma yanzu ban tabbatar ko akwai Allah ko ba bu shi ba, kuma ban damu ba."

A cikin shekaru 16 da jam'iyyar shugaba Recep Tayip Erdogan ta yi kan mulki, an samu karuwa a yawan makaratun sakandare na addinin musulunci a kasar Turkiyya.

Ya rika magana a kan bukatar ganin cewa matasa sun tashi da tarbiyya ta addinin musulunci.

Sai dai a cikin makonnin da suka gabata, 'yan siyasa da malaman addinin musulunci sun rika tattaunawa a kan ko matasa musulmi masu ibada na barin addininsu.

A rana daya rayuwar Merve ta sauya, bayan ta tashi cikin damuwa ta kuma shafe sa'oi tana kuka amma ta yanke shawarar yin addu'a a kan lamarin.

Sai dai yayin da ta rika yin adduar sai ta fahimci cewa tana tababa game da wanzuwar Allah.

"Na dauka zan kamu da ciwon tabin hankali ko kuma zan kashe kaina," in ji ta. "Washe gari sai na fahimci cewa na rasa imanina."

Ba ita kadai ba ce ta tsinci kanta a cikin yanayi irin wannan.

An ambaci wani farfesa na cewa akwai gomman dalibai mata da suka zo wurinsa da kallabi a kansu wadanda suka bayyana masa cewa sun fara bin tafarkin wadanda ba su yarda da wanzuwar Allah ba a cikin shekarar da ta gabata ko fiye da haka.

Wannan layi ne

Bekir, dalibi mai karatun addini

Zanen hoton Bekir
Bayanan hoto, Wani zanen hoton Bekir

"In banda yanzu, a baya ni mai goyon bayan kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci ne irinsu kungiyar IS ko Al Qa'eda. A yanzu ban yadda da cewa akwai mahalicci ba.

Da farko na so na samu wata hujja a musulunci amma na kasa samunta . Daga nan ne na fara tantama game da wanzuwar Allah.

Na rika goyon bayan gangamin raya addinin musulunci da aka rikayi anan. Sai dai daniyya tana haifar da juyin hali . Sun so su rika yi mana danniya kuma daga nan ne muka fara nuna mu su cewa ba zamu amince da wannnan ba".

Wannan layi ne

Sai dai akwai wasu daliban da suka karbi wani addini daban bayan wadanda ba su yadda da cewa akwai Allah ba.

A wani taron bita da aka yi a Konya, daya daga cikin birane masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci a Turkiyya, an samu wasu da suka yi ikirarin cewa akwai wasu dalibai a makarantun addinin musulunci da suke barin addini suna koma wa wani addini daban da ake kira Deism, saboda abinda suka kira "sabanin da ake samu a cikin addinin Islama," a cewar rahotanin da aka wallafa a jaridun 'yan hammaya.

Addinin Deism ya samo asali ne daga al'adar Girkawa. Magoya bayan addinin sun yarda da cewa akwai Allah, amma ba su amince da sauran addinai ba.

Ministan Ilimi Ismet Yilmaz, ya ce ikikarin da wasu suka yi a taron bitar, magana ce da ba ta da tushe, kuma ya musanta rahotanni da ke cewa al'ummar kasar da aka yi wa tarbiyar addinin musulunci sun fara kauce wa hanya.

Sai dai duk da cewa babu wani bincike ko ra'ayoyin jama'a da aka tattara game da haka, amma an samu wasu da suka hadu da masu wannan ra'ayi kuma wannan ya isa ya janyo damuwa tsakanin shugabannin Turkiyya.

Wannan layi ne

Leyla, daliba a wata kwaleji

Wata rana ina tafiya a kan hanya domin na je kasuwa, Sai na cire kallabin da ke kaina kuma ban sake daura kalabin ba.

Mahaifina bai san cewa na karbi addinin Deism ba. Idan ya san da haka, ina fargabar cewa watakila zai hana kanwata kammala kartunta na digiri.

"Yar'uwarkii ta je jami'a kuma wannan shi ne abinda ya faru da ita."Watakila ya ce ba ni ne na fadawa Ubangiji ya halicce ni ba, a kan haka Ubangijina ba zai nemi wani abu daga wuri na ba . Ina da 'yanci na yi rayuwuta yadda nake so."

Wannan layi ne

Wani babban malamin addinin musulunci a Turkiyya wanda shi ne shugaban ma'aikatar addini ta kasar Ali Erbas, shi ma ya musanta yadda ake samun karuwa a yawan masu addinin Deism da kuma wadanda ba su yadda da wanzuwar Allah ba a tsakanin matasan kasar masu tsattsauran ra'ayi.

"Babu wani dan kasarmu da zai nuna dabi'a irin wannan," a cewarsa.

Shi ma Farfesa Hidayet Aybar, wannan malami wanda yana koyar da addini ne a wata jami'a ya nanata cewa, ba a samu wasu da suka koma addinin Deism ba.

"Deism ya yi watsi da koyarwar addinin musulunci. Bai amince da littafin Kur'ani mai tsarki ba, kuma bai yadda da Annabi Muhammad SAW ba.

Mabiya addinin ba su yadda da cewa akwai aljanna da wutar jahanama ba, da mala'iku da kuma ranar hisabi. Duk wadannan shika-shikan adinin musulunci ne. Addinin Deism ya yadda da wanzuwar ubangiji ne kawai," in ji shi .

A cewar wani masanin falsafa na addinin Deism, Ubangiji ya halicci duniya da kuma dukkanin halittu amma ba bu ruwansa da abubuwan da suke faruwa a rayuwar halitarsa kuma be giciyya masu kaidoji ko dokoki ba.

"Ina son na tabbatar maka da cewa babu masu irin wannan tunani a tsakanin matasanmu masu tsattsauran ra'ayi," in ji shi.

Wannan layi ne

Omer, wani ma'aikacin gwamnati da aka kora daga aiki

Zanen hoto
Bayanan hoto, Zanen hoto

Ni tsohon ma'aikacin gwamnati ne.Bayan yunkurin juyin mulkin soja da bai yi nasara ba da aka yi a shekarar 2016, aka kore ni daga aiki .

A baya ni mai tsatsauran ra'ayi ne wanda yake goyon bayan manufofin jam'iyya mai mulki.Lokacinda aka kore ni sai da na rika tambayar Ubangiji a kan dalilin da yasa hakan ta faru da ni.

Hakan ta sa na shiga cikin wani mawuyacin hali. Koda yake har yanzu ban karbi addinin Deism ba. Fatana shi ne na inganta alakar da ke tsakanin na da addinin musulunci amma ban san ko hakan zai yiwu ba.

Wannan layi ne

Sai dai kungiyar wadanda ba su yadda da wanzuwar Allah ba a Turkiyya ta yi ammanar cewa akwai kuskure a bayyannin farfesa Aybar kuma sun yi ikirarin cewa a cikin limamin addinin musulunci akwai wadanda basu yadda da wanzuwar sa ba

"A nan akwai shirye-shiryen da ake gabatarwa a talibijin inda ake muhawara a kan matakin da ya kamata a dauka a kan wadanda ba su yarda da wanzuwar Allah ba," a cewar kakakin kungiyar, Saner Atik.

"Akwai wasu da ke cewa ya kamata a kashesu, a yankasu gunduwa-gunduwa," in ji Saner Atik.

"Abu ne da ke bukatar kwazo ka fito ka ce kai ba ka yadda da Ubangiji ba a yanayi irin wannan.

Akwai wasu mata da suka saka nikabi wadanda suka bayyana cewa ba su yarda da wanzuwar Allah ba amma a cikin sirri, sai dai ba za su iya cire nikabinsu ba saboda suna tsoron iyalinsu da kuma sauran al'umma."

Mun sake haduwa da Merve a karo na biyu a gidanta. Mun gaisa ba tare da ta rufe gashinta da kallabi ba.

Ta amince ta rika barin gashinta a bude a cikin gida ko da ya kasance cewa akwai maza a wurin.

"Sai da na ji wani iri a lokacin da na hadu da wani namiji ba tare da kallabi ba," in ji ta.

"Amma yanzu na saba da haka, kuma ta haka ne nake son na bayyana kaina a yanzu."

An dai sauya dukkannin sunnayen mutanen da aka yi hira dasu wadanda basu yarda da wanzuwar Allah ba, da kuma mabiya addinin Deism