Ruwan sama ya kashe mutum 20 a Kenya

Rahotanni daga Kenya na cewa madatsar ruwa ta fashe sakamakon tsananin ruwan sama da aka tafka a cikin daren Alhamis, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 20.

Al'amarin ya faru ne a garin Solai da ke arewa maso yammacin Nairobi.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce zuwa yanzu ta ceto rayukan mutum 39, yayin da wasu daruruwa suka rasa matsugunansu.

Jami'an yankin sun ce kawo yanzu ba za su iya tantance adadin asarar da aka tafka ba.