An gano zuciyar Sarauniyar Faransa da aka sace

Hoton yana nuna akwatin zinari wanda ya kunshi zuciyar Sarauniya Anne ta Brittany, wadda fadar Blois ta gano, a tsakiyar Faransa, a matsayin wani bangare na bikin tunawa da shekaru 500 na rasuwarsa ta, ranar 21 ga watan Maris 2014.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Akwatin zinarin na rike da zuciyar Anne, sarauniyar Faransa wanda ta rasu fiye da shekara 500 da su ka wuce.

'Yan sandan a Faransa sun gano wani akwatin zinari da ke dauke da zuciyar daya daga cikin wata jaruma, wadda aka sace daga wani gidan adana kayan tarihi a makon jiya.

Akwatin wanda yake dauke da kayayyaki mallakin Sarauniya Anne, an kera shi ne a karni na 16.

'Yan sanda sun kama mutanen biyu a ranar Asabar kuma sun kai su inda aka binne akwatin kusa da birnin San Nazaire da ke yammacin kasar.

Anne kadai ce macen da aka taba nada wa Sarauniyar Faransa sau biyu.

An ce tana daya daga cikin mata mafiya arziki, kuma aka fara yi wa alkawarin auren Yarima Edward na Ingila.

Amma yariman ya yi batan-dabo lokacin yana yaro, tare da dan uwansa Richard - an zargin kawunsa King Richard III da sanadiyyar bacewarsu.

Daga baya Anne ta auri 'yan gidan sarautar Faransa guda biyu, Charles VIII a 1491 sannan kuma dan uwansa Louis XII a shekarar 1498.

Akwatin zinarin yana da nauyin Gram 500 da siffar zuciya, yana kuma da rubutun tsohon harshen Faransanci a jikinsa.

Hukumomin kasar sun bukaci a dawo da akwatin, don sun yi imani da cewa barayi ba su fahimci muhimmancin tarihin zuciyar ba, wanda aka kubuta daga narkewa bayan juyin juya halin Faransa a shekarar 1789.