Barcelona ta buga wasanni 39 ba a doke ta ba a La liga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta kafa sabon tarihi a La liga bayan ta doke Valencia a karawar mako na 32 inda ta buga wasa 39 ba tare an samu galabarta ba.
Luis Suarez da Philippe Coutinho ne suka ci wa Barcelona kwallo biyu a ragar Valencia, yayin da Dani Parejo ya rama wa Valencia kwallo daya a bugun fanareti ana mintinan karshe.
Barcelona ta shafe tarihin da Real Sociedad ta kafa na buga wasanni 38 ba tare da an doke ta ba a kakar wasa ta 1979/80.
Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya yaba da rawar da 'yan wasansa suka taka, musamman bayan Roma ta fitar da su a gasar zakarun Turai.
Yanzu Barcelona tana da maki 82 a saman teburin La liga, tazarar maki 14 tsakaninta da Atletico Madrid da za ta fafata da Levente a ranar Lahadi.
Barcelona na iya daukar kofin La Ligar bana kafin fafatawar hamayya da za ta yi da Real Madrid a ranar 6 ga Mayu.
Kuma ga alama abin da Barcelona ta sa a gaba a yanzu shi ne a kammala La liga ba tare da an doke ta.
A karshen mako mai zuwa ne Barcelona za ta kara da Sevilla a wasan karshe na Copa del Rey.










