Buhari ya ce Gaddafi ne ya bai wa makiyaya makamai, Amnesty ta ce an rage yanke hukuncin kisa

Buhari ya ce Gaddafi ne ya bai wa makiyaya makamai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zargi tsohon shugaban Libiya Mu'ammar Gaddafi da bai wa makiyaya makamai a yankin Yammacin Afirka.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya aike wa manema labarai a ranar Laraba.

An rage yanke hukuncin kisa - Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce adadin mutanen da a ke yankewa hukuncin kisa a duniya ya ragu a bara, idan a ka kwatanta da shekarar 2016.

Kungiyar ta ce hakan zai share fage wajen soke yanke hukuncin kisa kwata-kwata.

An sace wani baturen Jamus a Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce an sace wani Bajamushe da ke gudanar da ayukan jin-kai a kusa da iyakar Mali.

A cewar ministan shari'a kuma Antoni-Janar din kasar, 'yan bindiga a kan babura ne suka sace mutumin mai suna, Joerg Lange, a garin Inates da ke yammacin kasar.

Farfesa ya 'nemi yin lalata da dalibarsa'

Hukumomin Jami'ar Obafemi Owolowo da ke garin Ile-ife ta ce ta kafa wani kwamitin domin bincikar sahihancin wata hirar waya da aka nada wadda aka ace tsakanin wani malamin jami'ar ne da wata daliba.

A cikin hirar an ji namijin ya nemi macen ta amince ya yi lalata da ita har sau biyar domin ya kara mata makin da zai sa ta ci jarrabawa saboda ta fadi.

Wanda ya lashe gasar cin attaruhu ya bige a asibiti

Wani mutum wanda ya ci attaruhun da ya fi ko wanne yaji a duniya a wajen gasar cin barkono ya samu kansa a gadon asibiti bayan da ya hadu da wani gigitaccen ciwon kai mai kamar saukar aradu a ka.

Mutumin mai shekara 34 ya ci attaruhun ne safurin Carolina Reaper a wajen agasar da aka yi a birnin New York na Amurka.

Buffon ya ce alkalin wasa ne ya zalunce su

Kyaftin din Juventus Gianluigi Buffon ya ce alkalin wasa ya zalunce su a wasan da Real Madrid ta fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turai.

Alkalin wasan na Ingila Mark Oliver ya bai wa Madrid fanareti a mintin karshe bayan da Mehdi Benatia ya ture Lucas Vazquez, sannan kuma ya bai wa Buffon jan kati.

Ronaldo ya ce gaban shi ya fadi kafin ya buga fanareti

Cristiano Ronaldo ya ce sai da ya kwantar da hankalinsa sosai kafin ya buga fanaretin da ya ci ana daf da tashi daga wasansu da Juventus.

Fanaretin da Ronaldo ya ci ne ya taimakawa Real Madrid kai wa zagayen daf da na karshe a gasar zakarun Turai.

Bidiyo: Ba ni da kawa a matan Kannywood - Umma Shehu

Karanta karin wasu labaran

Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.