Sanatoci nawa ne ke goyon bayan Buhari, an yi 'ruwan kudi' a bikin 'yar Dangote
An bai wa Buhari lambar yabo ta 'boge'
Cibiyar The King Center, wacce ke adana tarihin fitaccen bakar fatar nan na Amurka, marigayi Martin Luther, ta nesanta kanta daga lambar yabon da aka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Asalin hoton, Bashir Ahmed Twitter
An kashe fiye da mutum 60 a Zamfara
Mazauna wani kauye da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun ce barayin shanu sun kashe sama da mutum 60 a kwanaki biyu da suka wuce.

Asalin hoton, zamfara government
An hana El-Rufai karbar bashin naira biliyan 126
Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gabatar mata ta cin bashin $350m (naira biliyan 126) daga Bankin Duniya.
'Yan majalisarsun yi watsi da bukatar karbo bashin ne "saboda Kaduna ita ce jiha ta biyu da ta fi yawan bashin da ake bin ta".

Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT
Karanta karin wasu labaran
Kalli bidiyonmu na yau
Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.








