Najeriya: An kashe fiye da mutum 60 a Zamfara

Bayanan sautiHira da wani ganau kan kisan Zamfara

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hira da wani ganau mazaunin garin ya yi wa BBC kan harin farko:

Mazauna wani kauye da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun ce barayin shanu sun kashe sama da mutum 60 a kwanaki biyu da suka wuce.

Sun shaida wa BBC cewa mutum 15 aka kashe a harin farko.

Sauran kuma an kashe su ne a wasu jerin hare-hare da barayin suka kai lokacin da ake jana'izar mutanen farko da suka hallaka, inda mutum uku ne kawai suka rayu.

A ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai makon da ya gabata a jihar, ya umarci jami'an tsaro su kawo karshen miyagun laifuka da ake aikatawa a jihar.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya gaya wa BBC cewa a lokacin da suka shiga garin, sun sami gawawwaki uku na mutanen da maharan suka kashe.

Wannan layi ne

Ba a daina kashe mutane ba

An kashe mutane da dama a sabbin hare-haren jihar Zamfara

Asalin hoton, zamfara government

Bayanan hoto, An kashe mutane da dama a sabbin hare-haren jihar Zamfara

An dade ana fama da kashe-kashen mutane a jihar Zamfara, al'amarin da ya addai mazauna yankin.

Sai dai duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi har yanzu lamarin bai sauya ba.

A baya ma wani dan majalisar dattawa da ke wakiltar jihar ya zargi Gwamna Abdul'aziz Yari da cewa ya san masu kai hare-haren, zargin da gwamnatin jihar ta musanta.

A ranar 10 ga watan Maris din nan ma, gwamnatin jihar ta tabbatar da kashe Buharin Daji, wanda shi ne jagoran barayin shanun da suka addabi jihar da hare-hare.

Amma ga dukkan alamu kisan nasa bai sa an daina kashe mutane ba.