'Yaran' Buharin Daji sun kashe sojoji 11 a Kaduna

IDRIS KPOTUN FACEBOOK

Asalin hoton, IDRIS KPOTUN FACEBOOK

Bayanan hoto, Ana zaton harin na ramuwar gayya ne

Wasu 'yan bindiga sun kashe sojoji 11 a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

BBC ta samu tabbacin faruwar lamarin na ranar Talata da dadare.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar, wadanda ake zargi yaran jagoran barayin shanun da aka kashe a jihar Zamfara Buharin Daji ne, sun yi kisan ne a matsayin ramuwar gayya.

Wata majiya ta shaida wa kafar yada labarai ta PRNigeria cewa mutanen, dauke da muggan makamai, sun abka wa sojojin da ke aiki a shingayen bincikensu wanda ke Doka, wadda ke tsakanin Funtua da Birnin Gwari sannan suka kashe sojojin nan take.

An jibge gawarwakin sojojin da aka yanka a wani dakin ajiye gawarwaki.

Rahotanni sun ce tun da fari maharan sun abka wa yankin Maganda inda suka kai harin ramuwar gayya saboda kisan Buhari Tsoho, inda suka raunata 'yan kato da gora tara.

Bayan nan ne suka nufi Kampanin Doka da ke kan iyaka da hanyar da za ta kai ga kauyukan Gwaska da Dansadau inda suka sake kai hari wanda shi ne ya yi sanadin mutuwar sojojin.

A farkon watan Maris ne gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Buharin Daji, jagoran barayin shanu da suka addabi jihar da hare-hare.

Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris

Asalin hoton, ZAMFARA GOVERNMENT

Bayanan hoto, Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris