
Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari a makarantar sakandaren mata ta kwana a Dapchi jihar Yobe da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Asalin hoton, Isaac Linus Abrak
Dalibai mata 110 da aka sace a baya baya nan a Nijeriya ya nuna cewa har yanzu Boko Haram na tasiri sosai a kasar, duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta karya lagwon kungiyar.
Wakilin BBC kan harkokin tsaro a Afrika, Tomi Oladipo ya yi nazari kan karfin mayakan Islama masu tada kayar baya da kuma alakar da ke tsakaninsu da kungiyar IS.
Shin ko IS tana da hannu gameda 'yan matan da aka sace?
Sai dai duk da cewa kai tsaye ba ta da hannu a cikin alamarin, amma wani bangare na kungiyar Boko Haram da ya yi wa IS mubaya'a shi ne yake da alhakin sace dalibai 'yan matan, da kuma matan jami'an 'yan sanda kuma malaman jamiar Maiduguri da aka sace a bara a yankin arewa maso gabashin kasar.

Asalin hoton, Reuters
An fi sanin kungiyar da sunan kungiyar IS da ke yammacin Afrika watau ISWAP, kuma manufar sunanta ita ce ta nuna yadda IS ta fadada ayuikanta daga gabas ta tsakiya zuwa arewacin Afrika.
IS ta san da zaman kungiyar, inda Abu Musab al-barnawi shi ne jagora.
An yi ammanar cewa shi ne 'dan mutumin daya kafa kungiyar Boko Haram, Mohammed Yusuf , wanda aka kashe yana tsare a hannun 'yan sanda a shekarar 2009.
IS na taimaka wa ISWAP wajan tsara farfaganda mai kyau.
Bayan wannan, ba bu wata alaka kai tsaye tsakanin bangarorin biyu.
Shin mene ya kawo baraka tsakanin Boko Haram ?

Asalin hoton, Boko Haram
Duk da cewa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya yi wa IS mubaya'a a shekarar 2015, amma bangaren da ya balle na adawa da yadda yake tafiyar shugabancinsa da kuma ayuikan kungiyar, ciki har da yara kanana da ake amfani da su a matsayin 'yan kurnar bakin wake da kuma harin da ake kai wa musulmi.
Ba bu cikakkaken bayani kan ko wani bangare na kungiyar BH ne ya fi tasiri amma dukkaninsu na ayuikansu a tafkin Chadi.
Bangaren da ke karkashin jagorancin Shekau ya fi tasiri a yankin arewa maso gabashi da ke kusa da kasar Kamaru, ya yinda ISWAP ta fi tasiri kan iyakar jamhuriyar Nijar.

Gwamnati ta ce ta yi amfani da wasu hanyoyin wajan ganin an sako 'yan matan Dapchi ciki har da wata kasa da ba bu ruwanta da wata kungiyar agaji ta kasa da kasa da kuma masu shiga tsakanin da aka yadda da su.
Sai dai akwai wani almari da ya faru a baya kafin wannan.
A bara ne bangare da ke karkashin Abubakar Shekau ya sako wasu daga cikin dalibai yan mata Chibok su 276 da aka sace a shekarar 2014 tare da taimakon gwamnatin Switzerland da kuma kungiyar agaji ta Red cross.
Sakinsu na cikin matsayar da aka cimma na yin musayyar fursononi ,inda gwamnati ta saki wasu kwamadojin kungiyar Boko Haram.
Bayan dalibai 'yan matan Dapchi da aka sako, minista yada labaran Nijeriya, Lai Mohammed ya shaidawa sashin turanci na Focus on Afrika cewa gwamntin kasar na tattaunawa da mayakan BH a kan yadda zasu tsaigata bude wuta. Duk da cewa a baya shugaba Muhammadu Buhari ya nanata cewa ba zai tattauna da mayakan ba.
"Muna magana da su. Wannan shi ne dalilin da yasa 'yan matan da aka sace ya bamu mamaki," a cewar Lai Mohammed
Ya ce ba bu diyyar da aka biya ko furusononin da aka yi musanye da su.
Watakila gwamnati na ganin nasara da aka yi wajan sako 'yan matan Dapchi kan iya sa a dakatar da bude wuta .
Sai dai wannan ya yi hannun riga da manufar mayakan kungiyar BH na fada da gwamnati dominsu kafa daular musulunci.
A bana ne Nijeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru suka kadammar da kai farmaki kan Boko Haram .
An yi wa shirin lakabi da Operation Deep Punch 2 kuma rundunar sojin kasar ta yi ikikarin samun nasara .
Sai dai ba bu wata alama data nuna cewa zaa kawo karshen farmakin nan bada jimawa ba,duk da cewa gwamnati ta ce an dakatar da hare haren ne domin a bude hanyar da zaa dawo da 'yan matan Dapchi cikin koshin lafiya , wadanda mayakan BH suka ajiye a garin bayan wata guda da yin awon gaba da dasu.
Biyar daga cikin 'yan matan sun rasu lokacin da suke hannun 'yan Boko Haram . Akwai kuma kiritsa daya da ta ki musulunta wadda ba a sakota ba.

Asalin hoton, Reuters
Nasarar da sojoji suka yi ta sa an sake bude wasu hanyoyi, abinda ya sake dawo da hada hadar kasuwanci a yankin arewa maso gabashin kasar.
Sai dai wannan zai sa 'yan Boko Haram su iya tafiya cikin sauki kuma zasu iya koma wa yankunan da aka fatattakesu.
A sharhi na karshe , ba bu isasun sojoji da zasu yaki Boko Haram, wadanda kuma zasu iya gadi a kowani gari da kauye ko makaranta a yankin arewa maso gabashin Nijeriya , lokacinda da suka sako yan matan Dapchi sun gargade su akansu tabbatar basu koma makarantar boko ba.
An kuma kai wa kayan kungiyoyin agaji hari, kamar yadda muka gani a harin da aka kai wa Majalisar Dinkin Duniya a garin Rann a ranar 1 ga watan Maris..
A baya Abu Musab al-Barnawi ya yi Alla wadai da kungiyoyin agaji na kasashen yamma, ma su aikin jin kai ga wadanda da rikicin ya dai daita, inda ya ce suna kokarin maida musulmi kirista.
Ra'ayinsa ya nuna cewa ba bu alamar kawo karshen rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Nigeria.
Bayanan da kuke bukatar sani tun sace 'yan matan Dapchi