PDP ku dawo da kudaden da ku ka sace - Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga PDP da ta cika ladanta na neman afuwar 'yan Najeriya ta hanyar dawo da dukkan kudin da aka sace daga baitil malin kasar a lokacin da take mulki tsawon shekara 16.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar Talata a Abuja babban birnin kasar, Ministan Watsa Labarai da Al'adu Alhaji Lai Mohammed, ya kuma kalubalanci PDP da ta nuna lallai afuwar da take nema ta gaske ce ta hanyar sauya halayyarta.

Sanarwar ta ce: "PDP ta jagoranci wawushe lalitar gwamnati, irin wanda ba a taba yi ba a Najeriya ko kuma a ko ina a duniya.

"Don haka babban abun yi shi ne ba kawai ta dinga bayar da hakuri ba, dawo da kudin ya kamata ta yi. In ko ba haka ba to duk abun da take fada yaudara ce."

Gwamnatin ta fitar da sanarwar ne a matsayin mayar da martani kan wata sanarwa da tun da fari jam'iyyar PDP ta fitar, inda take neman afuwan 'yan kasar game da kura-kuran da ta tafka a lokacin da ta mulki kasar na tsawon shekara 16.

Jam'iyyar PDP ta ce ta nemi afuwan 'yan kasar ne saboda su ba ta goyon baya a jam'iyyar wadda a yanzu aka yi mata garanbawul.

Sai dai jam'iyyun biyu sun sha nunawa juna yatsa ta hanyar zargin juna da rashin tafiyar da kasar yadda ya kamata.

Amma sanarwar ta ci gaba da cewa: "Duk da matsalar rashin isassun kudade da take fuskanta, gwamnatin Buhari ta kashe makudan kudade wajen ayyukan more rayuwa da Shirin Tallafa Al'umma da sauran su.

"Dawo da kudaden da aka sace zai taimaka wajen aiwatar da wasu shirye-shiryen da kuma kyautata rayuwar 'yan Najeriya. Babu wani ban hakuri da ya fi wannan,' in ji sanarwar gwamnatin.

Alhaji Mohammed ya kuma tunasar da PDP da cewa: "Idan ka samu kanka a rami, to ka dakatar da tono," yana mai cewa irin hakan ce ta faru da PDP a wannan lokaci.

Ministan ya kara da cewa: "PDP ki sauya taku. Ki daina yin kafar ungula ga ayyukan gwamnatin nan, wacce take gyara kwamacalar da ki ka yi a baya. Ki daina munanan kalamai da zarge-zarge marasa tushe.

"Ki adawa mai ma'ana. Ki sanya muradun 'yan Najeriya fiye da son rai a lamuranki. Ki rage kwadayin son dawowa mulki. Ki ware lokaci na musamman wajen tuba, idan ki ka yi haka za a gafarta maki," a cewar Mista Mohammed.

Wasu masana dai a Najeriyar na ganin wannan sa-toka-sa-katsi da ake ci gaba da yi tsakanin manyan jam'iyyun kasar biyu, wani abu ne da ke jawo tsaiko wajen hada kai don ciyar da kasar gaba.

Karin labaran da za ku so ku karanta: