Liverpool za ta hadu da Manchester City a gasar zakarun Turai

Asalin hoton, Reuters
Manchester City zata hadu da Liverpool a zagayen daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai.
Liverpool ce dai ta doke Manchester City a premier a kakar bana a haduwar da suka yi a 14 ga Janairu, amma a watan satumba City ta lallasa Liverpool 5-0.
Liverpool ce za ta fara karbar bakuncin City a Anfield a ranar 4 ga Afrilu, kafin su sake haduwa a ranar 10 ga Afrilu a gidan City.
Wannan ne karon farko da kungiyoyin Ingila za su hadu a zagayen daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai tun haduwar Chelsea da Manchester United a kakar 2010-11.
Hada kungiyoyin biyu dai ya nuna cewa dole a samu kungiya daya daga Ingila a zagayen daf da na karshe.
Barcelona da ke jagorancin teburin La Liga an hada ta ne da Roma.
Sevilla kuma da ta fitar da Manchester United za ta hadu ne da Bayern Munich.

Asalin hoton, Reuters
Sauran kungiyoyin da aka hada.
Barcelona da Roma
Sevilla da Bayern Munich
Juventus da Real Madrid
Liverpool da Manchester City










