Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama wadanda ake zargi da kona Fulani a Benue
'Yan sanda a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya sun kama mutane da dama da ake zargi suna da hannu a kisan wasu Fulani bakwai da aka yi tare da kona gawarwakinsu.
A ranar Laraba ne wasu gungun mutane 'yan kabilar Tiv suka kashe Fulanin a garin Gboko.
A wata sanarwa da rundunar 'yan sanda jihar ta fitar ta ce ta samu labarin aika-aikar ne a ranar Larabar da misalin karfe 9.30 na safe, cewa al'amarin ya faru ne a tashar motar garin na Gboko.
"Nan da nan aka tura 'yan sanda wajen inda suka tarar da gawarwakin wasu maza bakwai da ba a gane ko su waye ba, amma dai 'yan kabilar Fulani ne," in ji sanarwar.
"An far musu ne aka kashe su sannan kuma aka cinnawa gawarwakinsu wuta a tashar."
Sanarwar ta kara da cewa: "Bayanan farko da aka samu sun nuna cewa mutanen da aka kashe din fasinjoji ne a wata mota mai zuwa garin Okene na jihar Kogi daga Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Tuni dai Gwamnan jihar Samuel Ortom da kwamishinan 'yan sandan jihar Fatai Owoseni, suka ziyarci wajen da abun ya faru don ganewa idonsu.
A yanzu haka dai an fara tuhumar wadanda aka kama da ake zargi da lamarin.
Kazalika rundunar 'yan sandan ta sha alwashin daukar mataki mai tsanani kan duk wanda aka kama da hannu dumu-dumu.
Tuni dai gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a garin Gboko, kuma ta sanya jami'an tsaro su sanya idanu sosai don gudun sake faruwar wani abu.
A baya-bayan nan rikici tsakanin makiyaya da manoma ya janyo asarar rayuka a jihohin Benue da Taraba da kuma Adamawa.
Rikicin yana daga cikin manyan kalubalen tsaro da kasar yanzu ke fuskanta, baya ga rikicin Boko Haram, da matsalar sacewa da garkuwa da mutane da rikice-rikicen kabilanci da na addini da suka addabi kasar.