Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nigeria: An sa dokar hana fita a garin Gboko na Benue
Gwamnatin jihar Benue wadda take tsakiyar Najeriya ta ce ta sanya dokar hana zirga-zirga daga dare zuwa safiya a garin Gboko daga ranar Laraba.
Gwamnan jihar Samuel Ortom ya ce sun dauki matakin ne saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a yankin, inda ya ce dokar za ta fara aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.
A ranar Laraba ne wasu gungun mutane 'yan kabilar Tiv suka kashe wasu Fulani bakwai a garin Gboko, kana daga bisani suka kona gawarwakinsu.
Al'amarin ya faru ne a ranar Larabar da misalin karfe 9.30 na safe, a tashar motar garin na Gboko.
Bayanan farko da aka samu sun nuna cewa mutanen da aka kashe din fasinjoji ne a wata mota mai zuwa garin Okene na jihar Kogi daga Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
A baya-bayan nan rikici tsakanin makiyaya da manoma ya janyo asarar rayuka a jihohin Benue da Taraba da kuma Adamawa.
Rikicin yana daga cikin manyan kalubalen tsaro da kasar yanzu ke fuskanta, baya ga rikicin Boko Haram, da matsalar sacewa da garkuwa da mutane da rikice-rikicen kabilanci da na addini da suka addabi kasar.