'Yan Kungiyar IS sun shigo Nigeria — Buhari

'Yan Kungiyar IS da ke ikirarin jihadi reshen yammacin Afirka, IWSA, sun shiga jihar Benue a Najeriya, inda aka yi kashe-kashe a kwanakin baya a wani rikici da ake tsammanin ya faru ne tsakanin manoma da makiyaya.

Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta ce bayanai da jami'an tsaro na ciki har da na farin kaya suka tattara sun nuna cewa 'yan kungiyar ta IS sun shiga jihohin tsakiyar Najeriya da kudu maso kudancin kasar da zummar yaki, domin kara tayar da hankali tsakanin kabilu da mabiya addinai daban-daban a kasar.

Wata majiya a fadar shugaban Najeriya ta ce an gano wannan ne bayan an kama wasu mahara da ake zargin Fulani makiyaya ne, da mayakan da gwamnati ke mara wa baya da kuma sauran masu tayar da kayar baya a jihar Benue.

Fadar gwamnatin shugaban Najeriya da ta tabbatarwa da BBC da labarin, ta kuma ce cikin wadanda suka shiga hannu a halin yanzu, akwai wadanda ba sa iya ko daya daga cikin harsunan Najeriya, sai dai Faransanci.

Wannan shi ne karon farko da jami'an tsaro suka tabbatar da cewa ISWA tana gudanar da al'amuranta a cikin Najeriya, kuma aka gano cewa ta kai wannan matakin na kitsa kai hare-hare a cikin kasar.Fadar shugaban kasar ta ce an kama masu tayar da kayar baya na ISWA a jihar Benue da Edo, musamman a garuruwan Akoko-Edo da Okpella da Benin da kuma Okene a jihar Kogi.

An samu bayanai da suka nuna cewa kungiyar tana yada akidarta domin ta samu matasan da za su yi mata aiki.

Kazalika kungiyar ta shirya kai wasu jerin hare-hare a lokacin bukukuwan Kirsimetin da ya gabata.

Sai dai rundunar tsaron Najeriya ta farin kaya (DSS) ta dakile shirye-shiryen kai hare-haren ta hanyar kama da yawa daga cikin masu tayar da kayar bayan.

Rahoton da aka mika wa fadar shugaban kasar ya nuna cewar ana fargabar yaduwar 'yan IS zuwa ko ina a fadin kasar.

Da aka tambayi mai magana da yawun fadar shugaban kasar, Garba Shehu, game da lamarin, sai ya tabbatar da cewa Shugaban Muhammadu Buhari ya samu rahotanni game da halin da ake ciki a Benue da sauran jihohin, kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi nasarar kama masu tayar da kayar baya da yawa a baya-bayan nan.

Dama dai Najeriya na fama da rikicin a yankin arewa maso gabashin kasar, inda kungiyar Boko Haram ke yawan kai hare-hare duk da cewa a baya-bayan nan gwamnati na kokarin murkushe su.

Baya ga rikicin Boko Haram kuma ana yawan samun matsalar rashin tsaro a wasu sassa daban-daban na kasar, kama daga satar mutane don samun kudin fansa zuwa rikici tsakanin manoma da makiyaya.